Yadda Ake Daukar Ciki – Sanin Yadda Ake Daukar Ciki muhimmin al'amari ne a rayuwar mace, wanda yake nuni da haduwar kwai a mahaifarki da maniyyin namiji. Wannan blog post zai yi muku bayani dalla-dalla gameda yadda ake daukar ciki, tun daga lokacin saduwa har zuwa lokacin da mace ke fahimta da kanta cewa ta dauki ciki. Za mu kuma tabo wasu tambayoyi da ake yawan yi game da ciki da daukarsa. Menene Daukar Ciki? Daukar ciki yana faruwa ne idan kwan mace a mahaifa ya gamu da maniyyin namiji, sannan kuma ya kafe a bangon mahaifa. Wannan yana faruwa ne lokacin ko bayan saduwar aure ko inda maniyyi ke shiga cikin farji kuma ya tafi har ya hadu da kwai a bututun fallopian. Matakan Yadda Ake Daukar Ciki – 1. Fitar Kwai (Ovulation) Kowace mace tana fitar da kwai sau ɗaya a kowane zagaye na wata. Wannan shine mataki na farko na yadda ake daukar ciki, yana faruwa ne tsakanin rana ta 11 zuwa ta 21 bayan jinin al’ada, bisa ga tsari da al'adar kowace mace. 2. Lokacin da Aka Fi Sauki...
Read love, romance, adventure novels complete on our platform