Yadda Ake Daukar Ciki –
Sanin Yadda Ake Daukar Ciki muhimmin al'amari ne a rayuwar mace, wanda yake nuni da haduwar kwai a mahaifarki da maniyyin namiji. Wannan blog post zai yi muku bayani dalla-dalla gameda yadda ake daukar ciki, tun daga lokacin saduwa har zuwa lokacin da mace ke fahimta da kanta cewa ta dauki ciki. Za mu kuma tabo wasu tambayoyi da ake yawan yi game da ciki da daukarsa.
Menene Daukar Ciki?
Daukar ciki yana faruwa ne idan kwan mace a mahaifa ya gamu da maniyyin namiji, sannan kuma ya kafe a bangon mahaifa. Wannan yana faruwa ne lokacin ko bayan saduwar aure ko inda maniyyi ke shiga cikin farji kuma ya tafi har ya hadu da kwai a bututun fallopian.
Matakan Yadda Ake Daukar Ciki –
1. Fitar Kwai (Ovulation)
Kowace mace tana fitar da kwai sau ɗaya a kowane zagaye na wata. Wannan shine mataki na farko na yadda ake daukar ciki, yana faruwa ne tsakanin rana ta 11 zuwa ta 21 bayan jinin al’ada, bisa ga tsari da al'adar kowace mace.
2. Lokacin da Aka Fi Saukin Daukar Ciki
Akwai kwanaki 5 zuwa 6 da ake kira “lokacin da mace ke da saukin daukar ciki.” Wannan lokacin yana gaf da lokacin da kwai ke fitowa. Idan aka sadu a wannan lokacin, akwai yiwuwar daukar ciki sosai.
3. Haduwar Maniyyi da Kwai
Bayan saduwa, maniyyin namiji yana tafiya daga farji zuwa mahaifa har ya hadu da kwai a bututun mahaifa. Idan sun hadu, suna samar da wata tsoka da ake kira da “zygote” wanda take komawa mahaifa domin kafewa.
4. Kafewa a Bangon Mahaifa
Wannan tsokar ta zygote yana raba kansa a hankali ya zama embryo, kuma yana tafiya zuwa mahaifa inda zai kafa kansa a bangon mahaifa. Wannan shine matakin da ke tabbatar da daukar ciki. Wato Yadda ake daukar ciki ya dogara ne da wannan mataki.
Alamomin Farko na Daukar Ciki
Mace na iya fara jin wasu canje-canje da ke nuni da cewa ta dauki ciki. Ga wasu daga cikinsu:
-
Rashin zuwa jinin al'ada
-
Jin kasala ko gajiya
-
Yawan fitsari
-
Ciwon nono ko kumburarsa
-
Jin jiri ko amai (musamman da safe)
-
Canjin yanayin jiki da hankali
-
Yawan zafi a jiki
Yadda Ake Tantance Ciki
1. Gwajin Ciki na Gida
Za'a iya amfani da kayan gwajin ciki da ake saya a chemist ko pharmacy. Ana yin gwajin da fitsari, musamman da safe domin samun sakamako mai inganci.
2. Gwajin Ciki a Asibiti
Za'a iya zuwa asibiti domin a duba ta hanyar gwajin jini ko ultrasound. Wannan zai tabbatar da ciki da kuma kimanin kwanakin da aka dauka.
Abubuwan da Ke Iya Hana Daukar Ciki
A wasu lokuta, mace tana iya fuskantar wahalar daukar ciki saboda wasu dalilai kamar:
-
Matsalar fitar kwai
-
Ciwon mahaifa ko bututun fallopian
-
Rashin Isasshen sinadarin hormones
-
Matsalar lafiyar maniyyin namiji
-
Matsalolin ciki da suka faru a baya
-
Wahalhalu da gajiya
Shawarwari Ga Masu Son Daukar Ciki
-
Ki lura da lokacin ovulation (zai fi kyau a yi amfani da calendar ko app)
-
A rage damuwa da samun gajiya sosai
-
Kar asha giya, ko taba sauran miyagun kwayoyi
-
Abinci mai kyau lafiyayye
-
A sadu da miji akai-akai musamman a lokacin da kwai ke yawan fita
-
Idan an jima ba'a samu ciki ba, a tuntuɓi likita
Tambayoyin da Ake Yawan Yi
1. Yaushe mace ke daukar ciki bayan saduwa?
Mace na iya daukar ciki cikin awa 24 zuwa 48 bayan saduwa idan maniyyin mijinta ya gamu da kwai.
2. Za a iya daukar ciki daga saduwa sau daya?
Eh, idan aka sadu a lokacin da mace ke da saurin daukar ciki, akwai yiwuwar ta dauki ciki daga saduwa sau daya.
3. Yaya ake sanin lokacin fitar kwai?
Akwai alamomi kamar fitar ruwa daga farji, zafi a ciki, ko amfani da na’urar gwajin.
Kammalawa
Ilimi akan yadda ake daukar ciki na daga cikin al’amuran rayuwa masu muhimmanci ga mata da ma’aurata. Fahimtar yadda tsarin yake da kuma sanin lokacin da mace ke da saukin daukar ciki na taimakawa sosai ga masu fatan samun ‘ya’ya. Idan kina da wata tambaya ko kike bukatar karin bayani, kada ki ji kunya ki tuntube mu ta email.