Maganin Hips Cikin Kwana Uku

Maganin Hips Cikin Kwana Uku:

Maganin Hips Cikin Kwana Uku

A yanzu, samun maganin hips cikin kwana uku yana da wahala, amma nayi iya abinda zan iya domin samun bayanai masu dacewa, a yau son cikakken kwankwaso mai cike da kyau da ɗaukar hankali ya zama wani abu da mata da yawa ke sha'awa. Ko dai kina son samun ƙarin kyan gani a jiki ko kuma don jin daɗin kanki, akwai hanyoyi da za su iya taimaka miki cika hips ɗinki cikin kwana uku kacal. Duk da cewa sakamako na dindindin yana ɗaukar lokaci, akwai matakan da za su sa jikinki ya fara nuna sauyi a cikin gajeren lokaci. Ga abubuwan kamar haka.


Abinci: Ginshiƙi Na Farko

Domin samun hips cikin kwana uku, yana da matuƙar muhimmanci ki kula da irin abincin da kike ci. Idan hips ɗinki basu da tsoka ko mai (fat), to dole ne ki fara da gina su daga ciki.


Kalar abincin da zasu taimaka miki sune:

  • Kwai: Ya ƙunshi furotin da sinadaran da suke gina tsoka. Cin kwai guda biyu da safe na iya taimakawa.
  • Avocado: Mai cike da healthy fats. Yana ƙara cika sassan fata da ƙarfafa fata.
  • Madara mai kitse: Zata taimaka wajen ƙara nauyi a jikinki wacce take zuwa kai tsaye hips da buttocks.
  • Dankalin turawa (sweet potato): Na cike da carbohydrates da ke sa kumburin jiki cikin sauri.
  • Kaza (chicken breast): Furotin mai kyau da ke taimakawa wajen cika hips da gina tsoka.

Shawara: Ki tabbatar kina cin abinci sau uku a rana tareda snacks masu amfani a tsakanin lokaci.



Magungunan Gida: Hadin Dake Aiki Da Sauri

Maganin gida ba wai sai ansha wahala ko tsada ba. Akwai hadaddun man shafawa da za su iya taimaka miki samun canjin hips cikin kwana uku.


1. Hulba da Man Zaitun

  • A haɗa garin hulba da man zaitun
  • A rika shafawa a yankin hips da safe da yamma.
  • A shafe a hankali na minti 10.
  • A bar shi a jikin na awa 1 kafin a wanke.

Me yasa yake aiki? Hulba na motsa jini a ƙarƙashin fata, sannan man zaitun yana kara laushin fata da ƙara mata kumburi.


2. Man Kwakwa da Habbatus-Sauda

  • A haɗa su daidai gwargwado.
  • A shafa bayan wanka da dare.
  • Ki lullube da zani ko wrap domin ya narke a fatar.

Fa’ida: Wannan haɗin yana sa fata ta cika da kyau, tare da rage bushewa da santsi.



Motsa Jiki: Na Cika Tsoka da Saurin Gaske

Yin motsa jiki a gida zai taimaka sosai wajen ganin sauyi cikin kwanaki ukun. Ba sai kina da kayan gym ba, ga wasu daga cikin manyan motsa jikin da ake buƙata:


Squats:

Zaki zauna kamar za ki zauna a kujera, sannan ki miƙe. Yi hakan sau 15 da safe da sau 15 da yamma.


Glute bridge:

Ki kwanta a bayanki, ki ɗaga ƙugu sama sannan ki dawo ƙasa a hankali. Yi sau 15 sau biyu a rana.


Donkey kicks:

Ki durƙusa ki ɗaga ƙafa sama kamar ki na dukan iska. Wannan na ƙarfafa sassan bayan hips da buttocks sosai.


Shawara: Ki tabbatar kina motsa jiki da safe bayan cin abinci, da kuma da yamma kafin ki yi amfani da man shafawa.



Sa Fata Laushi: Lalle da Yoghurt

Idan kina so hips ɗinki su yi haske da laushi, zaki iya amfani da lalle da yoghurt. Ki haɗa su ki shafe yankin hips, ki barshi na minti 30 sannan ki wanke da ruwan dumi. Wannan yana taimakawa wajen sabunta fata da ƙara mata ƙyalli da lafiyayyen kamanni.



Bacci Da Shan Ruwa:

Kada ki manta da shan ruwa da samun isasshen barci. Shan ruwa sosai yana taimaka wa fata ta kumbura sannan tayi kyau, yayin da barci na awanni 7 zuwa 8 ke bada dama ga jiki ya sarrafa abinci da tsoka cikin sauri. Rashin barci na hana duk wani cigaba da kike yi a jiki.


Rufewa 

Maganin hips cikin kwana uku shine bin abubuwan dana lissafa a sama, samun cikakken kwankwaso masu kyau da laushi cikin kwanaki uku na buƙatar bin ka'ida, juriya da kulawa. Idan kika yi amfani da magungunan gida, kika ci abinci mai amfani, kika motsa jiki da barci mai kyau, tabbas za ki fara ganin sauyi mai gamsarwa. Wannan sauyin na iya zama na wucin gadi, amma idan kika ci gaba da bin wadannan matakai, za ki samu sakamako mai dorewa cikin makonni ƙalilan masu zuwa.

Previous Post Next Post