Gyaran Nono Su Tsaya

Gyaran Nono: Su Tsaya Su Ciko

Gyaran Nono Su Tsaya

Gyaran nono su tsaya su ciko yana da kyau, sabida A al’ada, mata da dama na fuskantar sauyi a jikin su bayan haihuwa, shayarwa, ko idan shekaru na ci gaba wato girma yana kama ki. Daya daga cikin yankunan da hakan ke bayyana shi ne nono – yana iya sauya sifarsa, faduwa ko yin ƙanƙanta. Wannan na iya shafar kwarin gwiwa da yadda mace ke kallon kanta. Amma kyakkyawan labarin yau shine, akwai hanyoyi na kula da mace za ta iya bi domin gyaran nono su tsaya da cika, ba tareda tiyata ba.


1. Ta'ammali da Lafiyayyen Abinci

Abinci mai lahiya na taka muhimmiyar rawa wajen gyaran nono su tsaya yadda ya kamata. Idan ba'a sanyawa abinci sinadarai masu ciyar da fata da tsoka gaba ba, tofa gaskiya dole fata za ta yi rauni. Yana da kyau mace ta rika cin abinci lafiyayye, wanda ke da wadatar:


  • Protein: kamar kifi, kwai, wake, da nama mara mai.

  • Vitamin C da E: domin gyaran fata da kare ta daga lalacewa.

  • Healthy fats: kamar avokado, almonds, da man kwakwa suna taimakawa wajen cikar nono ta hanyar ƙara lafiyayyen kitse.


Shan ruwa mai yawa shima yana taimakawa sosai wajen ba fata danshi da ƙyalli.


2. Motsa Jiki na Musamman

Wato hajiya aikace-aikacen motsa jiki (exercises) suna taimakawa wajen ƙarfafa ƙirjinki a matsayinki na mace da kuma gyara sifar nononki. Misalan motsa jiki sun haɗa da:


  • Push-up: yana ƙarfafa tsokar ƙirji (chest muscles).

  • Wall press: kama bango ki tura hannunki a hankali kamar kina kokarin tura bango, a hankali- a hankali.

  • Arm circles: ki ɗaga hannuwanki sama ki na juyawa kamar agogo da kuma akasin haka wato gaba da baya.


Wadannan motsa jiki suna taimakawa wajen cike da tsayar da nono ta hanyar ƙarfafa tsokar ƙirji da kewayenta.


3. Shafawa da Tausar Nono

Akwai hanyoyin tausa (massage) da mace za ta iya amfani da su don inganta zagayowar jini a nono da sa su cika. kina iya amfani da:

  • Man zaitun

  • Man kwakwa

  • Man almond


Ki shafa daya daga cikin waɗannan man a nononki, ki dinga tausa da yatsunki a hankali a zagayen nono (circular motion) na tsawon mintuna 10 a kowanne gefe sau ɗaya ko sau biyu a rana. Wannan yana kara jini da sinadarai zuwa ga nono, yana inganta cikar su.


Wasu suna amfani da ice massage ( wato amfani da kankara, domin daskarar da nono na 'yan dakiku) domin ya ja fatar nono da tsokoki, sai su tsaya. Amma wannan hanya dole a yi da hankali don kada a matsa da yawa.


4. Yin Amfani da Ruwan Zuma da Madara

Wannan ma wata dabara ce ta gargajiya da mata ke amfani da ita wato hadin zuma da madara domin gyaran nono su tsaya, ko kuma zuma da kwai. Zaki haɗa ki shafa a nono, ki bar shi na mintuna 15–20 kafin ki wanke. Wannan na ƙara cikar fata da ƙyalli.


5. Sanya Rigar Nono Data Dace

Sanya bra mai kyau da ta dace da girman nononki yana da matuƙar tasiri wajen tsayar da nono. Kada a yawaita sanya bra marar ƙarfi ko marar daidaiton girma, domin hakan yana sa nono su fadi cikin kankanin lokaci.


6. Gujewa Rashin Motsa Jiki

Zama da yawa ba tareda motsawa ba, musamman bayan haihuwa ko cin abinci mai nauyi, na iya haifar da rage ƙarfi a ƙirji da kuma raunin fata. Motsawa a kai a kai da motsa jiki gaba ɗaya yana taimaka wa fata ta zauna da ƙarfi.



Kammalawa

Gyaran nono su tsaya su ciko ba sai da tiyata ba. Da kyakkyawan abinci, motsa jiki, tausa da mai, da kuma kiyaye wasu abubuwa a rayuwa, mace na iya samun nono tsayayyu da cika cikin ƙanƙanin lokaci. Abu mafi muhimmanci shi ne juriya da kulawa, domin waɗannan hanyoyin na dabi’ar yau da kullum ne, ba sa bada sakamako nan take, sai da lokaci da kuma kulawa.

Idan kina son inganta lafiyar jikinki gaba ɗaya, kula da nononki nasan ba zai gagara ba. Ki ba kanki kulawa – domin kin cancanta hajiya.

Previous Post Next Post