Alamomin Ciwon Koda:
Ciwon koda wata cuta ce da ke yawan shafar mutane a Najeriya da ma duniya baki ɗaya. Koda na taka muhimmiyar rawa a jikin dan Adam — domin ita keda ruwa da tsaki wajen tace jini domin fitar da abubuwa marasa kyau daga jiki, da kuma kula da daidaiton ruwa da sauran ma’adanai masu amfani a jiki. Idan Koda ta samu matsala, alamominta ba sa bayyana a lokaci guda sai cutar ta fara yin nisa. Wannan yasa yana da muhimmanci mutum ya fahimci alamomin ciwon koda tun da wuri domin samun kulawa kafin lamarin ya tsananta.
Menene Ciwon Koda?
Ciwon koda yana nufin lalacewa ko tsayawar aikin kodar mutum — wato kidney — wanda ke haddasa kasa tace jini yadda ya kamata. Wannan hakan na iya janyo taruwar gubobi a jiki, kumburi, saurin gajiya, da sauran matsaloli masu alaka.
Nau'ikan Ciwon Koda
-
Acute Kidney Injury (AKI) – Ciwo ne da ke faruwa da Koda cikin kankanin lokaci.
-
Chronic Kidney Disease (CKD) – Ciwo ne da ke faruwa a hankali na tsawon lokaci, yana ƙara ci sannu a hankali.
Alamomin Ciwon Koda Da Ya Kamata a Kula Dasu
1. Canji a Fitsari
-
Ragewa ko yawaitar fitsari ba yadda aka saba ba
-
Fitsari mai duhu ko ja ( me jini a ciki)
-
Fitsari mai kumfa (alama ce ta fitar protein)
-
Jin zafi ko ƙaiƙayi yayin yin fitsari
2. Kumburin Jiki
-
Kumburin kafa, idanu, hannaye da ciki shima na daga cikin Alamomin Ciwon Koda
-
Ciwon ciki ko gefen baya (inda kodar take)
3. Gajiya Da Kasala
-
Ji kamar ba ka da ƙarfi ko ƙarfin jiki koda yaushe na daga Alamomin Ciwon Koda
-
Saurin gajiya ba tare da ka yi wani aiki mai yawa ba
4. Rashin Cin Abinci
-
Kasala da rashin sha’awar cin abinci
-
Jin amai ko ciwon ciki bayan cin abinci
5. Karancin Sinadarai a Jini
-
Kasancewa da jini kaɗan saboda koda ba ta samar da isasshen erythropoietin wanda sinadari ne dake da alhaki wajen samar da sabon jini.
6. Jin Sanyi A Koda Yaushe
-
Ko da akwai dumi a waje, mai fama da ciwon koda na jin sanyi ko sanyi a gaɓoɓi
7. Ciwon Kai Da Matsin Lamba
-
Hawan jini yana ɗaya daga cikin manyan dalilan ciwon koda
-
Ciwon kai mai tsanani da yawan jin ciwon wuya ko baya suna na daga Alamomin Ciwon Koda
8. Karancin Hankali
-
Yayin da gubobi suka taru a jiki, yana iya janyo mantuwa, hauka ko rashin daidaiton tunani mutum
9. Fitar Jini a Cikin Fitsari
-
Idan ana ganin jini a fitsari sau da yawa, yana iya zama Alamomin Ciwon Koda
Dalilan Dake Janyo Ciwon Koda
-
Hawan jini (Hypertension)
-
Ciwon sukari (Diabetes)
-
Yawan shan magunguna ba tare da shawarar likita ba
-
Shan ruwa kaɗan
-
Yawan shan sinadaran guba kamar giya da taba
-
Cututtuka masu haddasa kamuwa da koda (kamar HIV, Hepatitis B & C)
Yadda Ake Tabbatar da Ciwon Koda
Idan kana fuskantar waɗannan alamomi da muka lissafo na Alamomin Ciwon Koda, wajibi ne ka nemi likita domin a gudanar da gwaje-gwaje kamar:
-
Blood test (Creatinine & Urea)
-
Urine test (Protein, blood)
-
Ultrasound ko CT scan don duba lafiyar kodarka
Yadda Za'a Kare Kai daga Ciwon Koda
-
Rage amfani da gishiri da yawa
-
Shan ruwa da yawa a kullum (akalla lita 2–3 a rana)
-
A guji yawan shan magani ba tareda izinin likita ba
-
A kula da cututtuka kamar su ciwon suga da hawan jini
-
A daina shan giya, taba da sauran abubuwan guba
-
Yin gwajin lafiya lokaci-lokaci
Tambayoyi da Ake Yawan Yi Akan Ciwon Koda (FAQs)
Shin akwai maganin ciwon koda na gida?
Akwai hanyoyi na rage radadin ciwon koda kamar daina shan gishiri, ko a kara shan ruwa da yawa, amma hakan ba zai maye gurbin likita ko asibiti ba. Idan alamomi sun bayyana, dole ne a je asibiti.
Ciwon koda yana warkewa?
Acute Kidney Injury yana iya warkewa idan aka gano shi da wuri. Amma Chronic Kidney Disease (CKD) yana buƙatar kulawa ta dindindin kuma ba ya warkewa gaba ɗaya, sai dai ana iya dakatar da cigaban cutar.
Kammalawa
Ciwon koda cuta ce mai tsanani da ke iya janyo mummunar illa ga lafiyar mutum idan ba a gane ta da wuri ba. Fahimtar alamomin ciwon koda yana da matuƙar muhimmanci domin gano matsala da wuri. Kada a jira ciwon ya tsananta kafin a je asibiti. Tsafta, shan ruwa da gwaje-gwaje na lafiya lokaci-lokaci na taimakawa wajen kare kai daga cutar ciwon Koda.