Siffofin Mace Mai Ciki:
Daukar ciki yana kawo sauye-sauye masu yawa a jikin mace, wanda a mafi yawan lokuta ana iya lura da su tun kafin mace ta yi gwajin ciki. Wadannan sauye-sauyen suna bayyana ta fuskar siffa, hali, da kuma canjin jiki gaba ɗaya.
A cikin wannan rubutu idan ubangiji ya amince, zan yi bayani dalla-dalla akan siffofin mace mai ciki, wato yadda siffofin mace ke canjawa a zahiri tun daga farkon daukar ciki har zuwa cigaba da rainonsa.
Menene Ma’anar “Siffofin Mace Mai Ciki”?
Kalmar “siffofi” a nan na nufin canje-canje da halaye da ke bayyana a jikin mace sakamakon daukar ciki. Wannan ya haɗa da canjin jiki, fuska, yadda take ji, da kuma halayenta na yau da kullum.
Muhimman Siffofin Mace Mai Ciki
1. Canjin Fuska
-
Fuska tana kara sheki saboda yawaitar jinin da ke yawo a jiki.
-
A wasu lokuta mace na iya samun kuraje a fuskar.
-
Fuskar kuma na iya duhu fiye da yadda take a da.
2. Kumburin Nono
-
Kumburin nonon mace na daya daga cikin Siffofin Mace Mai Ciki.
-
Tsakanin nonon yana iya kara duhu.
-
Mace na iya jin radadi ko zafi a nono.
3. Tashin Ciki ko Kumburi
-
Jiki yana nuna dan kumburi a ƙasan ciki.
-
Wannan yana faruwa ne tun daga makonni na farko.
4. Yawan Jin Kasala da Barci
-
Mace mai ciki na jin kasala da barci sosai musamman a farkon watanni.
-
Wannan yana faruwa ne sakamakon sauyin hormones.
5. Sauyin Hali da Tunani
-
Wasu mata na zama masu yawan saurin kuka ko saurin jin haushi.
-
Hakan yana faruwa ne sakamakon hormones da ke sauyawa a jiki.
6. Yawan Fitsari
-
Mace na jin fitsari sau da yawa fiye da yadda take yi a da.
-
Wannan yana da alaka da karin jini da ruwa a jikin mace mai ciki.
7. Amai da Zazzaɓi
-
Wasu mata na jin tashin zuciya da amai, musamman da safe.
-
Wannan yana nuna wani sabon canji a jikin da ke shirin ɗaukar jariri.
8. Saurin Jin Warin Abinci Ko Kamshi
-
Mace mai ciki na iya jin wari ko ƙiyayya da abincin da take so a baya.
-
Hakanan, zata iya fara sha’awar wasu sabbin abinci.
9. Canjin Girman Jiki
-
Ciki yana sa mace ta fara ƙara kiba musamman a ciki da nono.
-
Wasu na fara ganin canji a siffar jiki tun a wata 1 zuwa 2.
10. Fitar Ruwa Mai Launi
-
Wasu mata na iya ganin jini ko ruwa mai launin ruwan hoda, alamar cewa akwai kafuwar halitta a bangon mahaifa.
Shin Siffofi Kadai Suna Iya Tabbatar da Ciki?
A’a. Duk da cewa wadannan siffofin mace mai ciki suna nuna cewa mace na iya zama mai juna biyu, amma hanya mafi inganci ita ce yin gwajin ciki kamar:
-
Gwajin fitsari (Pregnancy Test)
-
Gwajin ciki a asibiti
-
Yin ultrasound don tabbatar da ciki da lafiyar jariri
Kammalawa
Siffofin mace mai ciki su ne canje-canje da mace ke fuskanta yayin daukar ciki. Wannan na iya kasancewa ta fuskar jiki, halayenta, da yadda take jin kanta. Amma duk da haka, babu wata hanya mafi sauki da inganci fiye da yin gwaji domin tabbatar da ciki.
Idan kina fuskantar wasu daga cikin wadannan siffofin mace mai ciki da muka lissafa a sama, zai fi dacewa ki nemi shawarar likita ko ki yi gwajin ciki domin samun tabbaci.