Yadda Ake Hirar Soyayya a Waya da Saurayi ko Budurwa
Zanyi muku bayani dalla-dalla akan yadda ake hirar soyayya a waya, babu ko shakka Soyayya na ɗaya daga cikin manyan abubuwan dake ƙara daɗin rayuwa. A zamanin yau, wayar hannu ta sauƙaƙa mu'amala tsakanin masoya – kama daga saƙonnin rubutu wato text messages har zuwa kiran murya har ma da kiran bidiyo. Sai dai kash Amma ba kowa ne ya san yadda ake hira mai daɗi da ta dace da soyayya a waya ba. Wannan shine dalilin da yasa nayo muku guzurin wannan post mai taken yadda ake hirar soyayya a waya, domin zamu tattauna yadda zaka iya gina dangantaka mai ƙarfi ta hanyar hira da budurwa a waya.
1. Farawa da Gaisuwa mai Daɗi
Yadda zaka fara hirarka nada matukar tasiri sosai. Kada ka fara da kalmomi gajeru kamar su “Hello” kawai. Kuyi amfani da kalmomi masu daɗi da nuna kulawa da nuna damuwa wa masoyi:
-
"Assalamu alaikum masoyiyata, ya ya kike?"
-
"Hmm, yau na dade ina tunaninki, ina fata kina cikin koshin lafiya?"
Wannan zai janyo hankalinta da jindaɗin cigaba da hira kai.
2. Tambayoyi Masu Taɓa Zuciya
Kada hirarku ta tsaya akan abubuwan yau da kullum kawai. Ku shigo da tambayoyi masu nuna kauna da nuna damuwa, kamar:
-
"Mene yafi faranta miki rai yau?"
-
"Ina fata kin huta nasan kinje makaranta yau ko?"
-
"Dama ace ina tareda ke yanzu babyna, da kinga soyayya mara misaltuwa, ina ji dake hubbyna"
Wannan na sa hirar ta zama mai ma’ana, ba kawai a wuce lokaci ba.
3. Mata Ko Masa Yabo
Kalmomi masu daɗi suna gina soyayya. Kada ka yi matsanancin yabo wato kada kayi yabo da yawa, amma ka fada gaskiya wacce take da ƙayatarwa:
-
“Muryarki tana kwantar min da hankali sosai.”
-
“Ina son yadda kike kula da dukan abinda na taba gaya miki – hakan yana bani mamaki.”
Yabo yana cike gibin nesa, yana sa masoyi ya ji daraja da kima.
4. Kada Hira Ta Zama Ƙunci
Wato abun nufi kada hirarku ta koma tambayoyi da amsoshi kamar ana cike fom:
-
Kai: Kina lafiya?
-
Ita: Lafiya.
-
Kai: Kin ci abinci?
-
Ita: Na ci.
Haka tana sa hira ta koma ba dadi. Malam ka zuba mata abun dariya, labarai, ko ƙananan abubuwan ban dariya domin ƙara nishaɗi da kuzari.
5. Gaya Mata Mafarkinka a Rayuwa
Ka gaya wa masoyiyarka abubuwan da kake mafarki. Wannan yana ƙarfafa soyayya sosai:
-
“Ina mafarkin ranar da zanyi tafiya tare da ke zuwa sauke farali.”
-
“Ina son in gina ahali mai tarbiyya tare da ke.”
fadin mafarki yana nuna tsananin niyyarka da cikar soyayya.
6. Kuyi Addu’a Ko Fatan Alheri a Ƙarshe
Kada ka rufe kiran waya haka kawai. Ƙare kiran da addu’a ko kalma mai daɗi yana saka masoyi jin daɗi da kewarka:
-
“Allah ya kiyaye min ke, ki kwanta lafiya masoyiyata.”
-
“Ina rokon Allah ya cika mana soyayyarmu da albarka kanwata.”
Zai sanyata ko shi cikin farin ciki har yasa wata gajeriyar hira ta biyo baya.
7. Ka Gane Lokacin Daya Kamata Kayi Shiru
Kada ka matsa da hira idan kana jin masoyiyarka/budurwarka bata da lokacin hakan a wannan lokacin wato ko tana wani aiki. Idan tace tana busy, kar ka dame ta. Hakan ma nuna soyayya ne: tausayawa lokacin juna.
Kammalawa
Hirar soyayya a waya ba sai da salon birgewa ba. Abin da ake buƙata shi ne gaskiya, kulawa, da iya zuba magana mai dadi a hankali. Ka rika mayar da hankalinka a lokacin hira, ka saurare ta da gaskiya, ka nuna damuwarka a aikace. Ta haka, soyayya zata ƙara zurfi har ta zama mai ɗorewa.