Alamomin Zuwan Jinin Haila
Jinin haila wani abu ne da kowace mace ke fuskanta a rayuwarta, tun daga lokacin data balaga har zuwa lokacin daina haihuwarta. Kafin jinin ya zo, akwai wasu alamomin zuwan jinin haila da ke nuna cewa al'ada tana gab da zuwa, kuma sanin waɗannan alamomi na taimakawa wajen shiryawa da kuma fahimtar yadda wasu halaye na jikin mace ke wakana.
A wannan blog post mai taken alamomin zuwan jinin haila, za mu duba duk wasu halaye ko alamu da mace ke iya ganewa ko ji a jikinki idan jinin al'ada yana shirin zuwa, dama yadda ya bambanta daga mace zuwa mace, da kuma abubuwan da zaki iya yi domin rage tashin hankali dama ciwo gaba ɗaya a lokacin.
1. Canjin Halayya
Ɗaya daga cikin alamomin farko na zuwan jinin haila shine canjin halayen mace. Kina iya fara jin damuwa taba gaira ba dalili, yawan ɓacin rai, ko rashin nutsuwa ba tareda dalili mai karfi ba. Wannan yana faruwa ne saboda canjin sinadaran hormones a jikin mace, kamar estrogen da progesterone.
🌸 Misali: Zaki iya jin kina so kiyi kuka ko kuma kiji ɓacin rai ko da ba'a miki komai ba.
2. Ciwon Ciki Ko A Baya
Jin zafi a ƙasan ciki ko baya, wanda wasu ke kira “ƙarin ciki” ko “tsantsar ciki”, yana ɗaya daga cikin shahararrun alamomin zuwan jinin haila. Wannan ciwon wasu lokutan na iya farawa kwana ɗaya zuwa uku kafin jinin al'ada ya bayyana.
💡 Shawara: Kina iya amfani da magungunan rage ciwo (kamar paracetamol) idan ya yi tsanani.
3. Kumburi da Jin Ciki Ya Cika
Wasu matan na iya jin cikin su yana kumbura ko kafin haila. Wannan kuma yana faruwa ne sakamakon taruwar ruwa a jiki, wanda ke faruwa daga sauyawar hormones shina.
🥦 Ki guji yawan shan gishiri a abinci ko wasu abin sha masu suga da yawa.
4. Yawan Jin Yunwa Ko Rashin Ci
Wasu lokutan mace tana ji tana yawan son cin abinci, musamman kayan zaki kamar chocolate, yayin da wasu kuma ba sa son cin abinci koma su dinga jin amai. Wannan ma yana daga cikin alamomin sauyin jiki kafin zuwan jinin haila.
🍫 Ba laifi bane jin sha’awar cakulet ko wani abu mai zaki – amma yana da kyau ki kula da abinci mai lafiya.
5. Canjin Fatar Jiki Ko Fuska
Yana faruwa fuska na iya samun kuraje ko canjin launi – musamman ga matan da ke da fata mai saurin samun tabo ko kuraje. Wannan yana daga cikin alamomin zuwan jinin haila.
🧴 Ki dinga wanke fuska da sabulun da ya dace da fatarki, ki kuma guji shafa duk wani mara kyau ko tsafta a fuskarki.
6. Yawan Fitsari da Kumburi a Nonuwa
Kafin haila, mace na iya jin nononta sun kumbura, sun yi zafi ko sun matse, har ma ta rinƙa yawan zuwa toilet. Wannan canji ne da ke faruwa daga hormones kafin haila.
🧘♀️ Ki rika saka bra mai laushi mara matsewa, ki kuma sha ruwa sosai domin rage kumburi.
7. Rashin Barci Ko Yawan Gajiya
Alamomin zuwan jinin haila na iya haɗawa da rashin samun isasshen barci, ko yawan jin gajiya duk da ba wani aiki kika yi mai yawa ba. Wannan yana faruwa ne sakamakon jiki na ƙoƙarin daidaita sinadarai.
☕ Ki guji shan abin sha masu caffeine da dare kuma ki kula da lokacin hutu (soft drinks masu caffeine sune: kamar Coffee, Coca-Cola, Passion, Dew, Pepsi da Predator.
8. Sauyin Jini
A ƙarshe, ana iya ganin ƙaramar fitar fari ko jini kaɗan a gaban mace, kafin jinin haila ya fara sosai. Wannan sauyin na daga cikin manyan alamomin zuwan jinin haila da ke nuna cewa al'ada tana tafe bada jimawa ba.
Bambancin Alamomi Tsakanin Mace Da Mace
Ba kowace mace ke fuskantar irin waɗannan alamomi dana lissafa a sama ba. Domin wata na iya jin ƙasa da 3 cikin 8, wasu kuma na iya jin su duka. Hakanan, alamomin zuwan jinin haila na iya bambanta daga wata zuwa wani watan a mace ɗaya.
Yadda Za Ki Kula da Kanki Idan Kin Fahimci Alamomin Haila
-
Ki shakata: Ki huta sosai idan kin fara jin alamomin.
-
Shirya pad ko tampons: Don kada ya kama ki a tsaka da tafiya.
-
Ki dinga rubuta lokacin al’ada: Wannan yana taimaka miki ki fahimci yadda jikinki ke aiki.
-
Ki dinga tuntubar likita: Idan alamomin sun yi tsanani fiye da kima, musamman ciwon ciki ko rashin barci.
Daga Karshe..
Sanin alamomin zuwan jinin haila yana taimaka wa mace wajen shirya masa da kuma fahimtar jikinta. Idan kina kinga waɗannan canje-canje a jikinki, kada ki damu – alama ce cewa jikinki yana aiki yadda ya kamata.
Kada ki manta: Idan kin kula da canjin al’ada ko alamomin fiye da yadda kika saba, yana da kyau ki nemi shawarar likita.