Gyaran Gashi da Ruwan Shinkafa

Gyaran Gashi da Ruwan Shinkafa –

Gyaran Gashi da Ruwan Shinkafa

Idan muna magana akan kula da gashi ta hanyar dabi’ar yau da kullum da mace zata iya bi, to ɗaya daga cikin dabarun da ke ƙara shahara a duniya shine amfani da ruwan shinkafa. Wannan tsohuwar dabara ce da mata a China da Japan suka daɗe suna amfani da ita domin tsawaita gashinsu da ƙarfafa shi. Amma menene ruwan shinkafa ke yi da yasa yake aiki haka?


Meyasa ruwan shinkafa ke da amfani?

Ruwan shinkafa yana cike da sinadarai masu amfani waɗanda ke taimaka wa lafiyar gashi da fatar kai gaba daya. Wasu daga cikin muhimman fa'idar ruwan shinkafa ga gashi sun haɗa da:

  • Yana hana faduwar gashi ta hanyar ciyar da tushen gashi.

  • ƙarfafa gashi, yana hana shi yankewa ko tsinkewa.

  • Sanya gashi ya yi laushi da sheƙi.

  • Yana taimakawa wajen tsawaita gashi cikin karamin lokaci.

  • Yana gyara gashi da ya lalace sakamakon sinadarai ko wanka da ruwan zafi.


Yadda ake haɗa ruwan shinkafa na gyaran gashi

Akwai hanyoyi guda biyu da suka fi shahara wajen hada ruwan shinkafa – hanyar ta normal da kuma hanyar fermentation (wato tsami ko muce rubewa kadan).


1. Hanya ta Normal Farko (Ba tsami kenan):

  • Wanke shinkafa (1/2 kofi) da ruwa.

  • Zuba ruwa (kamar kofi 2), ki bar shinkafar ta jiku na mintuna 30 zuwa 60.

  • Tace ruwan, ajiye shi a kwalba ko kwano mai kyau.

  • Wannan yana da sauƙin hadawa kuma zaki iya amfani da shi nan take.


2. Hanyar Fermentation (Ta tsami):

  • Kibi matakan farko kamar yadda nayi bayani a sama.

  • Bayan kin tace ruwan, ki ajiye shi a wuri mai dumi na awanni 12–24 har ya fara ɗan ɗaukar wari wato ya dan fara rubewa.

  • Wannan hanyar tana ƙara yawan sinadarai masu amfani da inganci a cikin ruwan.


Tips: Idan warin ruwan shinkafa ya yi yawa wato tayi tsami da yawa, to zaki iya ƙara zuba dan lemon tsami ko turaren ƙamshi (essential oil) kamar lavender ko tea tree.

 

Yadda zaki yi amfani da shi

Bayan wanke gashi da shampoo, zaki iya zuba ruwan shinkafa kai tsaye a cikin gashinki yayin da yake da ɗan danshi. Ki murza ya shiga duk ya kamata a kanki domin sinadarai su shiga sosai.


Bar ruwan a cikin gashi na tsawon mintuna 20 zuwa 30, sannan ki wanke shi da ruwa mai ɗan ɗumi. Hakanan, zaa iya amfani da shi a matsayin leave-in spray (wato fesawa) sau ɗaya zuwa sau biyu a mako, musamman idan kina da gashi mai bushewa.


Shin ruwan shinkafa yana da illa?

Ruwan shinkafa ba shi da illa ga yawancin mutane, amma yana da kyau ki gwada shi a ƙaramin yanki na gashi ko fata kafin amfani dashi gaba ɗaya, musamman idan kina da fata mai laushi ko mara karfi. Idan gashinki ya fara bushewa ko ya zama mai ƙauri, ki rage yawan amfani da shi zuwa sau ɗaya kawai a mako zai fi.



A ƙarshe...

Gyaran gashi da ruwan shinkafa hanya ce mai sauƙi, arha, kuma mai ɗorewa wajen gyaran gashi. Bata wani buƙatar siyan kayayyaki masu tsada domin hadawa, kuma yana iya kawo canji mai kyau idan ana amfani da shi akai-akai. Idan kina neman hanyar da za ta ƙarfafa gashinki da kawo karfingashi, to na baki wannan hanya kyauta Yar'uwa.

Previous Post Next Post