Yadda Ake Buɗe Account din Opay Cikin Sauƙi a (2025)
A yanzu, Opay na daya daga cikin shahararrun manhajojin hada-hadar kuɗi a Najeriya. Ana amfani da shi wajen aika kuɗi, karɓa, biyan kuɗin wutar lantarki, ruwa, data, POS da sauransu. Idan kai sabon mai amfani ne da opay, to babu shakka wannan rubutu nawa zai koya maka yadda ake buɗe Opay account cikin sauƙi, kai dai kawai kabi matakan ta zan kawo a kasa.
Menene Opay?
Opay wata manhaja ce da ke taimakawa mutane wajen gudanar da harkokin kuɗi ta wayar hannu. Tana bayar da sabis kamar:
-
Aikawa ko karɓar kuɗi
-
Biyan kudin NEPA, ruwa, DSTV da sauransu
-
Tura kuɗi zuwa sauran bankuna, misali; Zenith ko Acces bank
-
Samun katin ATM na Opay
-
Yin POS domin cire kudi a zahiri
-
Aikin agent (wato wakilin Opay)
Abubuwan Da Kake Bukata Domin Buɗe Opay
Kafin ka fara kokarin budewa, ka tabbatar kana da:
-
Smartphone (kirar Android ko iPhone), saboda karamar waya wacce bata daukar manhaja bata yi
-
Lambar waya (wacce kake amfani da ita yau da gobe, misali MTN, Airtel, Glo, ko 9mobile)
-
Data a wayarka ko ka jone da Wifi
-
ID (katin shaida) – kamar NIN wato katin dan-kasa, voter ID (katin zabe), da sauransu idan kana so ka haura matakin farko na amfani da opay, Level or Tier 1
Matakan Yadda Ake Buɗe Opay
1. Sauke Manhajar Opay
-
Ka shiga Play Store ko App Store
-
Ka rubuta “Opay” a search bar, sannan kayi searching
-
Bayan ya bayyana ka danna “Install” sannan ka jira ya gama sauka
2. Buɗe Manhajar
-
Bayan sauka, bude app ɗin
-
Danna “Open Account” ko “Sign Up”
3. Shigar da Bayanan Ka
Za a tambaye ka abubuwa kamar haka, kabi a hankali ka shigar:
-
Lambar wayarka
-
Zasu tura maka OTP ta message (lamba guda 6) sai ka rubutasu a gurbin da suka bayar a manhajar
-
Shigar da sunan ka, shekarar haihuwa, da kuma lambar sirri (PIN, lambobi ne guda hudu)
Ka sani: Lambar PIN shine kalmar sirri da zaka rika amfani da ita domin cire kuɗi ko kuma tura kudi a koda yaushe.
4. Zaɓi Matakin Account
Opay suna da Levels: Akwai
-
Level 1: Aiki da kudi kadan – wannan ba saida katin shaida ba
-
Level 2: Ana buƙatar NIN, BVN ko wani katin shaida
-
Level 3: Ana buƙatar cikakken bayaninka da tabbacin komai da komai a kanka
5. Ƙaddamar da Account ɗinka
-
Bayan ka cike komai, zaka shiga cikin manhajar a matsayin mai account
-
Zaka ga balance dinka, zaka iya aikawa, ko a turo maka kuɗi, da dai sauransu
ACCOUNT NUMBER DINKA itace LAMBAR WAYARKA
Menene Bambancin Lambar PIN da Lambar Password a Opay?
PIN shine lambar sirri guda hudu da zaka saka domin tiransifa din kudi, shi kuma PASSWORD lambobi ne guda shida da zaka dinga amfani dasu a duk lokacin da zaka shiga manhajarka ta Opay, wato kana shiga suna tambayarka. Kada ka bayyana PIN ko PASSWORD ɗinka ga kowa. Ka tabbatar kana amfani da lambobin da ba za a iya canko su da sauƙi ba.
Na sani cewa da yawa daga cikin mutane suna amfani da da shekarar haihuwarsu a matsayin PIN bama na Opay kadai ba harma da sauran bankuna, to gaskiya a gujewa yin hakan saboda tsaro.
Abubuwan Da Zaka Iya Yi Da Opay
-
Aika kuɗi daga Opay zuwa Opay ko Banki
-
Karɓar kuɗi daga POS ko abokai da yan-uwa
-
Biyan bills – NEPA, DSTV, Glo, MTN
-
Cire kuɗi a shagunan POS
-
Samun Opay ATM card
-
Yin ajiyar kuɗi
-
Aiki a matsayin Agent
Shawarwari:
-
Ka sabunta app ɗinka lokaci zuwa lokaci wato update daga Playstore
-
Ka kunna Face ID ko Fingerprint domin karin tsaro
-
Kada ka karɓi saƙo daga mutumin da baka sani ba, wani yace kayi kaza ko kaza, ko yace ka tura masa wani abu na opay dinka ko menene, ku sani ma'aikatan Opay basa taba tambayar wani abu daga gareka na sirri.
Kammalawa
Buɗe Opay account abu ne mai sauƙi idan kana da waya da lambar sadarwa. Yana da amfani musamman ga masu sana'a, ɗalibai, da duk wanda ke son gudanar da kuɗi cikin sauri da aminci. Idan kana buƙatar Opay Card ko kana son zama Opay Agent, duk zaka iya yi daga cikin app ɗin ko kayi amfani da Opay Business App.