YADDA AKE SAMUN KUƊI TA OPAY (2025 GUIDE)
Kamfanin Opay ya zama daya daga cikin hanyoyin samun kuɗi cikin sauƙi a Najeriya. Baya ga kasancewa manhaja ta turawa da karɓar kuɗi, Opay yana ba masu amfani damar kasancewa da riba ta hanyoyi daban-daban. Idan kana neman hanyoyi masu sauƙi kuma na halak domin samun kuɗi ta Opay, wannan rubutun nawa, dama kai na rubutawa, domin zai bayyana maka duk yadda zaka yi.
Menene Opay?
Opay manhaja ce ta wayar hannu da ke bawa mutane damar yin hada-hadar kuɗi, tura da karɓar kudi, biyan bills (NEPA, DSTV), sayen data, da ma amfani da POS. Har ila yau, tana bawa masu amfani dama su zama agent wato wakilansu ko su yi ajiyar kuɗi da riba (savings with interest).
HANYOYI 7 NA SAMUN KUƊI TA OPAY
✅ 1. Zama Wakilin Opay (POS Agent)
Wannan itace hanya mafi sauƙi da mutane ke samun riba. Idan ka zama Opay agent, zaka iya:
-
Turawa customer kuɗi
-
Cire masa kuɗi ka bashi Cash
-
Cajin customer yana kamawa ₦100–₦500 kawai ya danganta da wurin ne
-
Samun commission duk wata daga Opay
Riba: Ana iya samun ₦30,000–₦500,000 a wata, ya danganta da yawan abokan cinikayyarka da kuma location din shagonka.
✅ 2. Referral Bonus (Gayyato Sabbin Masu Amfani)
Opay yana bada lada idan ka gayyato sababbin masu amfani da app dinsu. Idan ka tura musu lambar gayyata (referral code), zaka samu kuɗi idan suka buɗe account da kuma yin amfani da app ɗin.
Riba: Ana samun ₦500 ko fiye da haka idan abokinka ya karbi gayyata yayi register.
✅ 3. Ajiyar Kuɗi da Riba (Opay Savings)
Opay yana da wasu cibiyoyin ajiyar kuɗi wanda suke bada riba idan kayi amfani dasu kamar:
-
OWealth – zaka iya ajiye kuɗi kuma ka rika samun kashi 15% na interest a shekara.
-
Target Savings – zaka yi ajiyar kuɗi domin cimma wani buri kamar siyan mota ko gida kafin ka gama tarawa, suna baka riba.
Riba: Idan ka ajiye kamar ₦10,000 na tsawon wata 12, zaka iya samun fiye da ₦1,500 riba. Kaga kenan idan ka ajiye miliyan 1 zaka samu 150k.
✅ 4. Sayar da Katin Data da Airtime
Zaka iya amfani da app ɗin Opay domin:
-
Siyar da airtime, wato katin kira
-
Siyar da MTN, Airtel, Glo, da 9mobile data
Riba: Zaka iya ƙara ₦50–₦100 akan kowanne data ko recharge. Idan wani ya siya a wajenka.
✅ 5. Biyan Bills Ga Mutane
Mutane da dama suna zuwa wajen wakilai wato agent domin biyan kudin NEPA, ruwa, DSTV da sauransu. Idan kai wakili ne, zaka iya cajin su da ƙaramin ƙari kamar ₦100 ko ₦200 a kowanne biya.
✅ 6. Taimakon Kudi (Loan)
Ko da yake wannan ba hanyar samun kudi bace kai tsaye, amma Opay na bada karamin lamuni (loan) ga masu amfani da app. Zaka iya amfani da wannan domin inganta sana'a ko POS.
Misali, ka karɓi rancen ₦200,000 kayi amfani dashi wajen kasuwancinka – ka dawo da shi da riba bayan kayyadadden lokaci. Akwai sharuda da ka'idoji.
✅ 7. Zama Opay Card Agent
Zaka iya sayar da Opay ATM cards ga masu bukata, musamman idan kana da shago ko kana da mutane da ke son katin cire kudi. Ana iya cajin ₦1000–₦1,500 duk guda daya.
📊 SHAWARWARI DOMIN SAMUN NASARA A OPAY
-
Ka kasance mai yin aiki mai kyau da kuma gaskiya
-
Ka sani cewa asusun ka da PIN ɗinka nada muhimmanci – ka kare su sosai
-
Ka daure ka sabunta app ɗinka don amfani da sabbin hanyoyin samun kuɗi
-
Ka zabi wuri mai yawan mutane idan kana da POS
-
Ka rika gayyatar mutane domin samun referral bonus
✅ KAMMALAWA
Opay ba kawai manhaja bace ta aika kuɗi – wata babbar dama ce ga duk wanda ke son samun halal da sauƙi. Ko kai ɗalibi ne, mai sana’a, ko matar gida, zaku iya amfani da Opay domin ƙara samun kuɗi ta hanyoyi da dama kamar yadda muka bayyana.