Cikakken Tarihin Bello Turji Kachalla
Tarihin Bello Turji Kachalla, wanda aka fi sani da Bello Turji, ya kasance ɗaya daga cikin fitattun shugabannin 'yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya. Sunansa ya karade kafafen watsa labarai saboda yadda ya mamaye dazuka da kauyukan Zamfara, Sokoto da kewaye da ayyukan ta'addanci. Wannan rubutu nawa na yau na tarihin bello turji zai bayyana muku cikakken tarihinsa – daga asalinsa, zuwa dalilan da suka sa ya shiga aikata ta'addanci, da kuma irin tasirin da hakan ya yi ga yankin.Farkon Tarihi
An haifi Bello Turji a shekara ta 1994 a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara. Ya fito daga kabilar Fulani, kuma rayuwarsa ta farko ta kasance mai kyau, inda ya taso a matsayin makiyayi. Bai samu damar zuwa makaranta ba, musamman ta boko, saboda yanayin zamantakewa irin tasu ta fulani da suka tsinci kansu a ciki.
A cewarsa, matsalolin rayuwarsu sun fara tsananta ne lokacin da wasu 'yan sa-kai suka kwace shanun iyayensa tare da kashe wasu daga cikin 'yan uwansa. Wannan ya haddasa masa bacin rai ba kadan ba, kuma daga nan ya fara ganin cewa Fulani kamar su ba su da kariya daga doka da gwamnati. Wannan ne ya fara jefa shi cikin ra'ayin ɗaukar fansa da makami.
Shiga Duniyar Ta’addanci
Bayan wannan gagarumin raɗaɗi da ya fuskanta, Bello Turji ya shiga daji tare da wasu matasa da ke fushi da yadda ake musu. Ya zama ɗaya daga cikin fitattun shugabanni a cikin ƙungiyoyin 'yan bindiga da ke aikata fashi, garkuwa da mutane da kisa a sassan Zamfara, Sokoto, da Kebbi.
An danganta shi da hare-haren da suka hallaka daruruwan mutane, ciki har da kona motoci, kisan fasinjoji, da kai farmaki kan kasuwanni da masallatai. Wasu rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyarsa ta kashe kusan mutane 200 a cikin wata guda a wasu yankunan Zamfara da Sokoto.
Dalilan Aikata Laifuka – A Cewar Bello Turji
A wasu lokuta, Bello Turji ya bayyana cewa ba ya aikata laifuka don jin daɗin kansa ba, sai don ya rama abin da ya ce gwamnati da 'yan sa-kai suka yi wa mutanensa Fulani. Ya zargi gwamnati da kafafen yada labarai da nuna bambanci, da rashin kula da 'yan kabilarsa, musamman makiyaya.
A wata hira da ya taba yi da wakilai daga yankin, ya bayyana cewa yana shirye ya daina daukar makami idan gwamnati za ta samar da adalci, zaman lafiya, da hakkoki ga Fulani irinsu.
Yunkurin Sasanci da Janyewa
A cikin shekarar 2022, Turji ya saki wasu mutane fiye da 50 da aka yi garkuwa da su, yana mai bayyana cewa yana so a sami zaman lafiya. Ya kuma rubuta wasiƙu zuwa ga manyan jami’an gwamnati, yana roƙon a sasanta tsakanin Fulani da sauran al’umma.
Sai dai, duk da wannan yunkuri, dakarun soji sun kai farmaki a sansaninsa da ke cikin dajin Isa da Sabon Birni a Sokoto, inda aka kashe wasu daga cikin mabiyansa. Wannan ya sa ya ɓoye na ɗan wani lokaci, amma daga baya ya sake bayyana.
Shekarar 2025
A yanzu haka, rahotanni na nuna cewa Bello Turji ya sake bayyana a wasu sassan Sokoto, inda ake cewa yana tilasta wa wasu kauyuka su biya kudin haraji har Naira miliyan 25 domin kariya. Wannan al'amari ya kara bayyana cewa yana da cikakken iko a wasu yankuna, duk da ƙoƙarin gwamnati na dakile tasirinsa.
Sojojin Najeriya sun sha alwashin cafke shi, tare da bayyana cewa suna bin sawunsa kuma ba zai daɗe ba kafin a kama shi ko a kawar da shi daga hanyar.
Kammalawa
Tarihin Bello Turji ya ƙunshi ɓangare ne mai wahalar ganewa cikin rikicin da ke faruwa a yankunan Arewa maso Yamma. Ga wasu, yana wakiltar matsin lamba da kabilun Fulani ke fuskanta. Ga wasu kuwa, yana ɗaya daga cikin barazana mafi girma da ke haddasa rashin zaman lafiya da tabarbarewar tsaro.
Ko da yake akwai lokutan da ya nuna aniyarsa ta yin sulhu, abubuwan da ke faruwa a halin yanzu na nuna cewa har yanzu kalubalen tsaro a yankin na buƙatar babban shiri da daidaito daga dukkan ɓangarorin biyu.