Kukan Shagwaba

Kukan Shagwaba:

A cikin soyayya da zamantakewa, musamman tsakanin masoya ko ma’aurata, ana samun wasu halaye da ke kara dan karen dadi da nishadi a cikin soyayya. Daya daga cikin irin waɗannan halaye shine kukan shagwaba. Duk da cewa yawanci ana danganta kukan shagwaba da yara, amma a soyayya da zamantakewar aure, musamman tsakanin ma’aurata ko masoya, kukan shagwaba ya zama hanya ta nuni da shagwaba, fushi, ko kuma neman kulawa.


A wannan rubutu, zamu yi bayani dalla-dalla akan kukan shagwaba: ma’anarsa, dalilansa, yadda ake yinsa musamman ga ‘yan mata da matan aure, da kuma yadda namiji zai yi idan masoyiyarsa tana yi masa.


Ma’anar Kukan Shagwaba

Kukan shagwaba a soyayya ko aure yana nufin irin ɗan kukan nan da mace ke yi ko ta kwaikwaya domin ta jawo hankalin mijinta ko saurayinta, ko kuma don nuna cewa tana bukatar kulawa ko tausayi daga masoyinta wanda a yawancin lokuta ba hawaye a cikinsa.


Wannan kuka ba wai dole ne yana fitowa ne saboda ciwo ko wata babbar damuwa ba, amma yana bayyana ne a matsayin wani nau’i na shagwaba ko shagube domin a biyota da lallashi ko kulawa ta musamman.


Siffofin Kukan Shagwaba Na Mata

  1. Kukan shagwaba yana zuwa tareda murmushi ko rada.
  2. Baya zuwa da hawaye na gaskiya sosai.
  3. Ana yin kukan ne a lokacin da mace take so mijinta ko saurayinta ya lallashe ta.
  4. Wasu lokuta akan ga ‘yan shagwaba kamar fushi, amma fushin na soyayya ne.


Dalilan Dake Janyo Kukan Shagwaba

Kamar yadda kowa ya sani, mace nada tausayi da shagwaba a halittarta, musamman idan tana cikin soyayya. Ga wasu daga cikin dalilan da ke sa mace ta yi kukan shagwaba:


1. Neman Kulawa Daga Masoyi

Sau da yawa mace na yin kukan shagwaba idan tana ganin kamar mijinta ko saurayinta bai damu da ita kamar yadda take so ba.


2. Domin Jindadin Lallashi

Wasu mata na jindadin ganin masoyinsu suna lallashi da rarrashi idan sun fara kukan shagwaba.


3. Neman Tausayawa ko Hakuri

Idan tayi wani kuskure ko tana jin tsoron fushi, zata iya amfani da kukan shagwaba domin a sassauta mata hukunci ko fushi.


4. Neman Wani Abu

A wasu lokuta, kukan shagwaba hanya ce da mace ke bi domin ta samu wani abu daga mijinta ko saurayinta.


5. Shagube Na Soyayya

Wasu lokuta mace na yin kukan shagwaba ne domin kawai ta zame mata dabi’a a cikin soyayyarsu, domin kara dankon zumunci.


Yadda Ake Yin Kukan Shagwaba (Domin ‘Yan Mata Ko Matan Aure)

Ga ‘yan mata, amaren da matan aure da ke son yin kukan shagwaba ga masoyinsu ko mazajensu, ga yadda ake yinsa cikin sauki da bin hanya mafi kyau:


1. Zaɓin Lokaci Mafi Dacewa

Kada ki fara kukan shagwaba lokacin da masoyinki ko mijinki yana cikin damuwa ko aiki. Zaɓi lokacin da zai iya fahimta.


2. Yi Kuka Cikin Sanyin Murya

Yin kuka da rada ko lafazi cikin natsuwa yafi jan hankali fiye da ihu ko kururuwa.


3. Yin Murmushi Lokaci-lokaci

Zaki iya yin kukan shagwaba tareda dan murmushi domin kada ya dauka cewa kina cikin damuwa sosai — hakan na nuna cewa shagwaba kike yi, ba kuka na damuwa ba.


4. Kalli Masoyinki Cikin Tausayi

Idan kina kuka, kina kallon fuskar masoyinki ko mijinki cikin tausayi, zai fi sa shi ya fahimci cewa kina bukatar kulawa ko lallashi.


5. Yin Kuka Cikin Shagube

Zaki iya cewa: “Ka barni kawai, ai baka damu dani ba…” ko “Ni dai ba zan ce komai ba, shikenan nidai kawai…” Wannan zai janyo dariyarsa ko kulawarsa cikin sauki.


6. Kukan Da Lafazi

Wasu mata suna amfani da kalmomi masu ban dariya ko masu jan hankali kamar: “Ni dai bana so, zan yi.....…” Wannan yana nuna cewa shagwaba kike yi don kawai a lallashe ki.


Yadda Namiji Zaiyi Idan Masoyiyarsa Tana Yi Masa Kukan Shagwaba

Ga maza da suke cikin soyayya da mace mai shagwaba ko ‘yar kukan shagwaba, yana da muhimmanci su san yadda za su bi lamarin cikin sauki da fahimta. Ga yadda namiji zai yi:


1. Kada Ka Yi Fushi

Ka sani cewa kukan shagwaba wata hanya ce da mace ke amfani da ita don jawo hankalinka. Kada ka dauki lamarin da zafi.


2. Lallashi Da Tausayi

Mafi yawan lokuta mace tana yin kukan shagwaba domin tana son a lallashe ta. Ka zo kusa da ita, ka shafa kanta ko kafadarta, ka gaya mata kalmomi masu dadi.


3. Yi Dariya Ka Karɓa Da Wasa

Ka ce mata: “Toh bari na dauko handkerchief domin zan share maki hawayen kinji babyna…” Wannan kalmar zata sa ta yi murmushi ko dariya.


4. Tambayeta Me Take So

Kayi mata tambaya cikin raha: “Ke dai wallahi shagwaba ne dake … Me kike so ne, ?” Wannan yana sa ta yi dariya ta daina.


5. Kar Ka Kula da Kowane Kukan

Idan kukan shagwaban yayi yawa sosai har ya zama kamar rashin ladabi ko rashin girmamawa, ka iya jan hankalinta cikin nutsuwa.


Kammalawa

Kukan shagwaba wani abu ne mai kayatarwa a cikin soyayya da zamantakewar aure. Yana kara dankon zumunci, yana sa soyayya ta kara dadi idan an fahimci yadda ake amfani da shi yadda ya dace. Ga mata, yana daga cikin dabarun da ke kara birge masoyi ko miji, idan aka yi shi cikin hankali da nutsuwa.


Ga maza, fahimtar kukan shagwaba zai taimaka wajen gina kyakkyawar dangantaka da masoyiyarsu ko matansu. Amma dole ne komai ya kasance cikin hakuri, fahimta, da nishadi.


Idan kina son masoyinki ya nuna kulawa sosai gareki, zaki iya yin kukan shagwaba, amma kada ki yishi da yawa ko a lokacin da bai dace ba.

Previous Post Next Post