Shin Gishiri Na Maganin Sanyi?
A tsakanin al’umma, musamman a Najeriya da yankunan Arewa, mutane da dama suna amfani da gishiri a matsayin maganin gargajiya domin maganin cututtuka daban-daban, ciki har da sanyi. Sau da dama zaka ji ana cewa “gishiri na maganin sanyi”, ko kuma zaka ga ana hada ruwan gishiri ana wanke baki ko hanci da shi. Amma mecece gaskiyar wannan magana? Shin gishiri na maganin sanyi ne ko kuwa al’ada ce kawai?
A cikin wannan rubutu, zan duba wadannan abubuwa:
- Menene sanyi a fannin lafiya?
- Yadda ake amfani da gishiri wajen magance sanyi
- Amfanin gishiri wajen rage alamomin sanyi
- Illolin amfani da gishiri fiye da kima
- Shawarar masana lafiya
Menene Sanyi?
A fannin kiwon lafiya, sanyi kalma ce da ake amfani da ita wajen bayyana cututtuka kamar mura, tari, zazzabi, ciwon makogwaro, da kuma yawan majina. A turance ana kiran sanyi da Common Cold ko Upper Respiratory Tract Infection (URTI).
Cutar sanyi tana faruwa ne sakamakon kamuwa da kwayoyin cuta irin su virus kamar rhinovirus da coronavirus.
Yadda Ake Amfani da Gishiri Wajen Magance Sanyi
Yawancin mutane suna amfani da ruwan gishiri mai dumi wajen:
-
Wanke Baki da Makogwaro: Ana zuba cokali daya na gishiri a cikin ruwan dumi, a motsa, sai ayi kurkura da shi. Ana yin hakan sau biyu zuwa uku a rana domin rage radadin ciwon makogwaro.
-
Shaƙar Hanci: Wasu lokuta ana amfani da ruwan gishiri mai dumi a wanke hanci domin cire majina da saukaka numfashi.
Shin Gishiri Na Maganin Sanyi?
Maganan Gishiri na maganin sanyi haka take amma bawai kai tsaye yake yi ba, illa iyaka yana taimakawa wajen rage wasu daga cikin alamomin sanyi kamar:
- Rage kumburi da radadin makogwaro
- Kawar da majina a hanci
- Taimakawa wajen tsabtace hanyoyin numfashi
SANNAN yana da kyau a fahimta cewa gishiri ba ya kashe kwayar cutar sanyi (virus). A zahiri, sanyi yana warkewa da kansa bayan kwanaki 5-10, koda an sha magani ko ba a sha ba. Ruwan gishiri kawai yana saukaka alamomin cutar ne don jin sauki.
Amfanin Gishiri Ga Lafiya:
- Rage kumburi a makogwaro
- Tsabtace hanci daga majina
- Yana taimakawa wajen kawar da wasu cututtuka na baki
Illolin Amfani da Gishiri Fiye da Kima
Idan aka yi amfani da gishiri fiye da kima, don tunanin gishiri na maganin sanyi, to zai iya haddasa:
- Bushewar makogwaro
- Zubar jini daga hanci
- Karin zafin makogwaro idan an yi amfani da ruwa mai zafi sosai
Haka kuma, shan gishiri da yawa a abinci na iya kawo matsalolin lafiya kamar hawan jini.
Shawarar Masana Lafiya
Masana lafiya suna shawartar cewa idan mutum yana fama da sanyi mai tsanani ko kuma alamomi kamar:
- Zazzabi mai tsanani
- Tari mai dauke da jini
- Ciwon kunne
- Jin zafi a jiki sosai
To, ya kamata a garzaya asibiti domin a duba lafiyar jiki gaba daya.
Kammalawa
Gishiri na maganin sanyi? eh taimakawa wajen rage wasu daga cikin alamomin sanyi kamar ciwon makogwaro da toshewar hanci. Amma ba maganin sanyi kai tsaye bane. Don samun lafiya da wuri, ana bukatar shan ruwa mai yawa, hutu, da cin abinci mai gina jiki. Idan sanyi yayi tsanani ko ya ki warkewa, kar ka yi jinkiri wajen zuwa asibiti.
Ku tuna: Maganin gargajiya yana da amfani, amma kada ya maye gurbin shawarar likita don tunƙahon gishiri na maganin sanyi.