Alamomin Mace Mai Ciki:
Daukar ciki wani muhimmin lokaci ne a rayuwar kowace mace. A wasu lokuta, mata na iya jin canji a jikinsu amma ba su da tabbas ko suna dauke da juna biyu ne ko a'a. Wannan yasa yana da muhimmanci mace ta san alamomin farko na daukar ciki, domin ta dauki matakan da suka dace.
A cikin wannan rubutu, za mu yi bayani dalla-dalla akan alamomin mace mai ciki domin taimaka wa mata su gane halin da jikinsu yake ciki tun da wuri.
Menene Ciki?
Ciki (wanda ake kira da juna biyu ko “pregnancy” a Turance) yana faruwa ne idan kwai daga mahaifa ya hadu da maniyyin da namiji, kuma ya kama a mahaifar mace. Wannan yana haifar da samuwar jariri a cikin mahaifa.
Alamomin Mace Mai Ciki (Na Farko-Farko)
1. Tsananin Jin Kasala ko Gajiya
Yawancin mata na jin gajiya sosai a makonni na farko na ciki saboda hauhawar sinadarin progesterone a jiki.
2. Rashin Zuwan Jinin Al’ada
Idan mace tana haila (al'ada) a kai a kai, kuma sai kwatsam ta daina zuwa, wannan na iya zama alamar ciki. Domin tsayawar zuwan jinin haila na daya daga Alamomin Mace Mai Ciki.
3. Jin Amai
A wasu matayen, ana samun jin amai musamman da safe. Wannan na faruwa tsakanin mako na 2 zuwa na 8 bayan daukar ciki.
4. Canjin Nono da Tsakaninsa
-
Jin zafin nono
-
Nonon ya kumbura ko canza launi
-
Tsakanin nono yana ƙara duhu
5. Yawan Jin Fitsari
Saboda jikin mace yana samar da karin jini da ruwa, hakan na sa ta yawan fitsari fiye da da.
6. Jin Zafi a Ciki
Wasu mata na jin dan kumburi a cikin ciki, musamman a ƙasan ciki.
7. Canjin Sha’awa a Kayan abinci
-
Yawan sha’awar wasu abinci (cravings)
-
Jin ƙiyayya da wani kamshi ko wani abincin
-
Sauyin hali kamar jin haushi
8. Jini Ko Fitar Ruwa Mai Launin Ruwan Hoda
A wasu lokuta, mace na iya ganin dan jini ko ruwa mai launin hoda — wannan na faruwa sakamakon kafuwar tsoka a jikin bangon mahaifa shima na daya daga cikin Alamomin Mace Mai Ciki.
9. Ciwon Kugu ko Baya
Wasu mata na jin zafin ƙasan baya ko ƙugu, musamman a farkon ciki.
10. Tashin zuciya da jin zafi a kirji
-
Jin zafin kirji ko ciki
-
Tashin zuciya ko amai bayan cin abinci
Yadda Ake Tabbatar da Ciki
Duk da wadannan alamomi na iya nuna cewa mace na da ciki, babu wata hanya mafi tabbaci fiye da yin gwajin ciki:
-
Pregnancy Test: Ana iya siyan su a pharmacy ko chemist. A yi amfani da fitsari domin sakamako mai inganci.
-
Ultrasound Scan: Ana amfani da shi a asibiti domin tabbatar da samuwar ciki da lafiyar jaririn.
Shin Kowace Mace Na Samun Wadannan Alamomi?
A’a. Ba kowace mace ba ce ke fuskantar duk wadannan alamomin na Alamomin Mace Mai Ciki da muka lissafa. Wasu na iya daukar ciki ba tare da wani alamomi da yawa ba, wato har sai cikin ya kai wata biyu ko uku. Haka kuma, alamomin na iya bambanta daga mace zuwa mace.
- Kammalawa
Sanin alamomin mace mai ciki yana da muhimmanci ga kowace mace, musamman wacce ke neman juna biyu ko kuma tana son kula da lafiyarta. Idan kina da wasu daga cikin wadannan alamomi, ki nemi a yi miki gwajin ciki domin tabbatarwa. Kula da lafiya da cin abinci mai kyau yana taimakawa wajen samun lafiyayyen ciki da kuma jariri.