Kalmomin Turanci Da Fassarar Hausa

Kalmomin Turanci da Fassarsu a Hausa –

Kalmomin Turanci Da Fassarar Hausa shine bayanin na yau. A wannan zamani da muka tsinci kanmu a ciki, yawan amfani da kalmomin Turanci yana ƙaruwa sosai a rayuwarmu ta yau da kullum, musamman a makarantu, ofisoshi, da kafafen sada zumunta. Amma da dama daga cikin masu amfani da harshen Hausa suna buƙatar fahimtar waɗannan kalmomi ta hanyar sauƙaƙa su zuwa Hausa. Wannan post ɗin zai kawo muku jerin muhimman kalmomin Turanci da fassarar su a Hausa, domin sauƙaƙa karatu, sadarwa da kuma fahimta.

Fa'idar Sanin Kalmomin Turanci da Fassarsu a Hausa

  • Sauƙaƙe fahimtar darussa a makaranta
  • Taimakawa wajen fassarar wasiƙu, sakonni da takardu
  • Inganta iya magana da rubutu a harshen Turanci
  • Taimako ga dalibai dama masu neman ilimi gaba ɗaya 

Jerin Kalmomin Turanci da Fassar a Hausa

Kalmomin Turanci Fassarar Hausa
BookLittafi
PenAlƙalami
SchoolMakaranta
ChairKujera
TableTebur
TeacherMalami/Malama
StudentDalibi/Daliba
LoveSoyayya
WaterRuwa
FoodAbinci
HouseGida
DoorƘofa
WindowTaga
LightHaske
CarMota
RoadHanya ko Titi 
MarketKasuwa
MoneyKuɗi
HappyMurna/Fara’a
SadBaƙin ciki

Kalmomin Turanci Masu Alaƙa da Zamani

English Word Hausa Meaning
ComputerKwamfuta
PhoneWaya
InternetYanar Gizo 
EmailImel
AppManhaja
Social MediaKafafen sada zumunta
ScreenshotHoton allo
DownloadSaukewa
UploadƊorawa 
PasswordKalmar sirri

Kalmomin Soyayya da Zamantakewa

Turanci Fassarar Hausa
HeartZuciya
FeelingJi (ko jin zuciya)
RelationshipDangantaka
MarriageAure
FriendAboki/Abokiya
TrustAminci
PromiseAlkawari
KissSumbata
HugRunguma
SmileMurmushi

Yadda zaka iya turanci a Sauƙaƙe

  • Kayi amfani da dictionary apps ko kamar su English Hausa Translator. (Wannan shafi namu na aiki domin ɗora Translator domin fassara magana daga turanci zuwa Hausa)
  • Rubuta sabbin kalmomi da fassara ka haddace da ƙwaƙwalwa
  • Yin amfani da su a cikin hira da rubutu a koda yaushe ba tare da jin kunya ba
  • Kalli fina-finan Hausa masu fassarar Turanci
  • Karanta littattafan da ke dauke da fassarorin harsunan guda biyu

Kammalawa

Kalmomin Turanci da fassarar Hausa suna da matuƙar amfani ga kowa da kowa – daga dalibi zuwa malamai, daga ma’aikaci zuwa ga ɗan kasuwa. Wannan ilimi yana buɗe ƙofofin fahimta, sadarwa da ci gaba na yau da kullum. Muna fatan wannan jerin zai taimake ka wajen ƙara ilimi da inganta maganarka da harsunan biyu a lokaci guda.
Previous Post Next Post