Sharhin Littafin Kwai Cikin Kaya na Bilyn Abdul
Kwai Cikin Kaya littafin marubuciya Bilyn Abdull ne yana ɗaya daga cikin fitattun littattafan Hausa da suka shahara a yan shekarun nan tsakanin masu karatu. Labarin kwai cikin kaya ya ƙunshi abubuwan da suka shafi soyayya, sirri, makirci, da kuma darussa masu ƙayatarwa. Bilyn Abdul ta wallafa littafin a shafukan yanar gizo kamar Kundintarihi.com.ng da Novels.com.ng, inda masu karatu ke samun damar karanta shi kyauta. Amma ayi sani cewa bani da tabbas cewa ita da kanta ta dora littafin a waɗannan kafofi illa iyaka Ni dai haka bincikena ya ganomin.
Ƙarancin Labarin Kwai Cikin Kaya a shafukan sada zumunta
Littafin Kwai Cikin Kaya yana bayar da labari ne akan rayuwar Jawaad, matashi mai kamun kai ga ladabi da biyayya, wanda ke fuskantar ƙalubale a rayuwarsa ta fuskar soyayyar dangantaka. A cikin labarin, marubuciyar ta bayyana yadda Jawaad ke mu'amala da Shahudah, wacce ta kasance kyakkyawar budurwa da ke da halaye masu ɗaure kai gamida rikitarwa. Labarin ya nuna yadda soyayya da kuma sirri ke haɗuwa, tareda bayyana yadda makirci da rashin fahimta ke iya shafar dangantakar masoya.
Jigo da Ma'anar Taken kwai cikin kaya:
Halayen Jaruman Cikin Littafin;
Jawaad: Shine babban tauraron littafin kuma ya kasance mai kirki da girmama kowa.
Shahudah: Budurwa mai kyau, wadda ke da alaƙar soyayya da Jawaad.
Gimba: Abokin Jawaad wanda ke taimaka masa a wasu lokuta.
Baba: Kakan Jawaad wanda ke da matukar tasiri a rayuwarsa.
Salo da Rubutun Littafin
Marubuciya Bylin Abdul ta yi amfani da harshen Hausa mai sauƙi mai saukin fahimta, tareda yin amfani da karin maganganu da misalai masu ƙayatarwa. Rubutun ya ƙunshi salo na ban dariya, tausayi, da kuma darussa masu amfani ga masu karatu.
Darussa Daga Littafin
Hakuri*
Juriya*
Sanin halayen mata musamman ga maza wanda suka soma soyayya kwanan nan.
girmama na gaba da kai.
Kammalawa
Kwai cikin kaya ko ban faɗa ba, gaskiya littafi wanda aka yi nazari sosai wajen rubutashi kuma dama ba sabon abu bane daga marubuciya Bylin Abdul domin tasan sirri da ilimin rayuwa yadda ya kamata. Ni dai shawara ta ga masoya a kodayaushe shine ku dinga riƙe amanar juna musamman ga yan'uwana maza kar ka batawa yar mutane lokaci kuma ka yaudareta. Nagode.