Skip to main content

Jarababben Namiji Complete Hausa Novel

Jarababben namiji complete hausa novel part 1

Jarababben Namiji Complete Hausa Novel

Jarababben namiji complete hausa novel littafi ne da muke fata zaku ilmantu da dashi domin sanin me ya kamata kuyi a rayuwa.

Shin yawan fada a cikin gida shike nuna cewa miji mai faɗa bashi da dadin zama?. Wannan tambaya ce wanda muka yi a shafin mu na facebook. Inda mata da yawa suka turo mana yanayin yadda suke zama da mazajensu na aure. Sai dai a cikinsu akwai wacce ta bamu cikakken labarin jarababben_namiji. Matar ta buƙaci mu sakaye sunanta amma duk da haka mun samu damar sanya sunanta a matsayin mawallafiyar wannan sabon labari namu mai cike da darussa wanda zasu amfane ku.

Tun ina karamar yarinya na kasance inada matukar kokari a makaranta, domin duk jarabawar da ake karshen zangon karatu nike zuwa ta ɗaya. Haka yasa iyayena da malamaina suke matukar sona sannan suna iya bakin kokarinsu domin suga sun samar min duk abinda nake bukata akan karatuna.

Kamar kowace rana, da safiyar yau Litinin mamana tayi min wanka, ta kimtsa ni sannan ta sakamin kayan makaranta. Muka fito zuwa falo inda na tarar da babana ya gama shiryawa shima zai wuce wajen aiki. Muka zauna muka yi karin kumallo, inda babana ke tambayata "Khadija idan kin girma me kike son ki zama ne" nayi murmushi nace "Daddy ina so na zama pilot" sai suka yi dariya, babana ya kalli mamana yace min "to ai mamanki so take ki zama likita" nayi dariya hmm da gaske mama?

A haka muna hira muka gama cin abinci, sannan muka wuce makaranta inda babana ya ajiye ni shi kuma ya wuce wajen aikinsa. Babana yanada rufin asiri dai dai kwarkwado domin ma'aikacin gwamnati ne, haka zalika mamana kuma kamar yadda al'adar malam bahaushe take da kuma koyarwar Islama kullum tana gida abinta, amma suna gudanar da kasuwanci ita da kawuna.

Yau shekara goma sha uku, domin na gama makarantar firamare zan shiga karamar sakandare, wato junior science. Yanzu na soma girma kyau na ya soma bayyana. duk da cewa ni ba fara bace amma irin yan'matan da ake cewa black beauty ce sannan inada tsayi gani da idanu dara dara masu kyau da jan hankali.

Babana akwai faɗa, amma yanada hakuri, irin wanda ake cewa jarababben namiji amma duk da haka Ni nasan yanada hakuri. Zai yi wuya ka ganshi yana faɗa akan wani abu amma idan aka kaishi bango to fa yana faɗa. Ni dai a tunanina jarababben namiji bashi da wani aibu.

Nayi wayo sosai domin yanzu da kaina nake zuwa makaranta, amma yanzu bana son zuwa makaranta, dalili kuwa na fuskanci mamana tanada juna biyu kuma bana so in ganta tana shan wahala, ina so inyi mata wanke-wanke inyi mata shara. Amma mama bata barina na zauna a gida, a haka nake tafiya ba dan ina so ba.

Jarababben namiji complete hausa novel last part 

Bayan wasu lokuta mamana ta soma nakuda muka tafi asibiti, bayan kamar awa biyu mamana ta haihu, sai dai nayi bakin ciki nayi kuka kamar zan mutu saboda mama ta rasa ranta yayin haihuwa. Haka muka dawo gida da kanina wanda aka sanya masa suna Halifa. Aka kaishi gidan kakata sannan ni kuma na cigaba da zuwa makaranta domin a lokacin na kai wajen shekara sha bakwai. Na girma ina iya yiwa kai na komai, daga ni sai mahaifina a gida haka muke rayuwarmu. Babana yana sona sosai nuna ina matukar kaunar mahaifina.

Rayuwa ta sauya sosai domin na soma jami'a ina yar shekara goma sha takwas, inda nake karantar microbiology program a Bayero University, wata rana na dawo gida da yamma, na zauna ina jiran baba. Har bayan magriba bai shigo gida ba, haka na zauna jiransa amma shiru, na dauki wayata na kira shi amma wayar a rufe, na kara gwadawa amma shiru.

Can bayan nayi bacci, sai gashi ya shigo ya ganni ina bacci, har ya samu mayafi ya rufeni saboda ana sanyi. Wannan dare shine ganin babana na karshe. Washe gari na tarar baba ya rasu akan gadonsa. Kamar zan mutu nayi kuka matuka. Bayan anyi masa sutura an kaishi an binne, da kwana bakwai na goma gidan kakata dama ita kaɗai ce sai ƙanina Halifa wanda kana ganinsa ka ganni kasan ɗan uwana ne na jini. Haka muka cigaba da zama a gidan kaka.

Na cigaba da karatuna domin kawuna ya dauki nauyi. Samari da dama sun nuna suna sona amma ban yarda na fara soyayya ba saida na samu mutumin kirki kuma saurayi mai aikin kansa sannan. Mun fara soyayya da Abdussalam baya da wata biyu kenan kuma yanzu ana zancen aurenmu nan da wata daya da rabi.

Ban sha wahalar rayuwa ba a baya, kuma haka na dinga addu'a na zauna lafiya da mijina. Sai dai wata matsala domin a yan kwanakin da muka yi soyayya da Abdussalam na fuskanci masifaffen namiji ne, domin ya fiye mita. Kuma gashi kishi amma yanada kirki kuma yana girmama dokokin Allah. Abdussalam ya bani shekara hudu a duniya kuma nima ina girmama shi domin ya cancanci hakan.

Jarababben namiji complete hausa novel
    Jarababben namiji complete hausa novel last 

Yanzu abubuwa da dama shi yake yimin kama daga suturata, takalmin sawa da dai sauransu, yanada hakuri sai dai jarababben namiji ne, idan jarabar ta motsa sai ya daina yimin magana. Amma baya daina zuwa wajena hakan ya tabbatar min da cewa Abdussalam yana sona. Yar uwa mai karanta wannan labari na jarababben namiji kiyi sani cewa a yanzu haka inada yara har guda da jarababben namiji, wanda ko da wasa bai taba azabtar dani ba.

Komai yana yi nida yarana bai rage ni da komai ba ko gidansa. Kawai abinda zaki yi idan kin fuskanci mijinki jarababben namiji ne to shine duk lokacin da kika kula yayi fushi to kada ki ƙara tunzura shi duk abinda yace kiyi to kiyi. Amma jarababben namiji yanada hakuri sai idan ai kaishi ne karshe ne yake faɗa kamar ba gobe.

Idan kuma kika ga ba zaki iya zama da namiji mai yawan faɗa ba, to kada ki soma aure domin da yawa daga cikin mazaje sunada faɗa sai dai wani yafi wani, abinda yake kawo faɗan kuwa shine nauyin iyali.

Comments

Popular posts from this blog

Littattafan Hausa Novel Complete Masu Dadi

Littattafan hausa novels masu dadi Littattafan hausa novel complete masu dadi gajeren sharhi. Allah mai girma da daukaka ya albarkaci garuruwan Hausawa da fasihan marubutan littafai daban-daban maza da mata. Wasu marubuta sunyi rubutunsu ne akan littafai na labaran ban dariya wasu kuma sunyi ne akan littattafan hausa novel masu dadi wanda ke ƙara basira wa masoya dama inganta al'adun Hausawa. Haka kuma ubangiji ya albarkaci ƙasar ta Hausa da masu karanta littafan Hausa Novels har complete din su.     Nayi mu'amala da mutane da dama wanda na fuskanci suna matukar neman Hausa Novels Complete domin ɗebe kewa dama samun nishadin rayuwa. Wannan ne dalilin da yasa na garzaya babbar ma'ajiyar Littattafai musamman romantic Hausa novels wacce muka fi sani a turance da digital Books store wato Arewa Books sannan nayi muku tsarabar jerin sababbi dama tsofaffin littafan Hausa wanda nake tunanin da izinin ubangiji zasu amfane ku ta hanyoyi masu yawa, idan da bukata zaku iya ziyartar sto...

Wasa Da Nonon Amarya A Daren Farko

Yadda Ake Wasa da Nonon Amarya a Daren Farko: Sanin abubuwan da ya kamata ayi a daren farko na aure ga amarya da ango yana da matukar muhimmanci, kasancewar hakan ne yasa mukai wannan rubutu na yadda ake wasa da nonon amarya a daren farko, wato domin ƙara danƙon soyayya da kauna tsakanin masoyan. Sanin yadda ake Wasa da nonon amarya a daren farko wani muhimmin abu ne da ya kamata ango ya sani, musamman idan an yi shi cikin natsuwa da kwanciyar hankali.  A cigaba da karatu cikin nutsuwa domin a wannan blog post, za mu bayar da dalilin da yasa da yawa daga cikin ma'aurata ke son yin wasa da matansu na sunna, sannan kuma zamu nuna yadda ake wasa da nonon amarya a daren farko, idan ma ku ba amare bane to fa wannan rubutu zai ƙara koya muku yadda ya kamata ku dinga yiwa matanku cikin sauƙi. Domin kuwa kodayaushe yana da kyau namiji yasan hanyoyin da zai kula da matarsa don tabbatar mata da jindaɗi da gamsuwa a kowane lokaci. Menene dalilin da yasa sanin hanyoyin da ake wasan da nonon am...

Sabbin Hausa Novels Complete

Sabbin Hausa Novels Complete –Hausa Novels 2025 Sabbin Hausa Novels Complete sun zama wani babban jigo a rayuwar masu karatu, musamman ma a wannan zamani da ake samun sababbin littattafan Hausa novels masu daukar hankali. Wannan rubutu namu na wannan rana zai kawo miki jerin Sabbin Hausa Novels Complete wanda aka saki a wannan shekara ta 2025, tareda cikakken bayanin inda zaki same su, har ma da abinda kowanne littafi ya kunsa. Sabbin Hausa Novels Complete na 2025 A cikin sabuwar shekarar 2025, marubuta littattafan soyayya na Hausa Novels da dama sun fitar da sababbin rubututtakansu masu kayatarwa da daukar hankali. Ga wasu daga cikin sabbin Hausa Novels Complete da suka samu karbuwa sosai: (1). Soyayyar Duniya – Aisha Ali Garkuwa Wannan littafi yana dauke da labarin soyayya mai cike da sarkakiya, shakuwa, da kuma sadaukarwa. Yana koyarwa mai karatu yadda masoya ke shawo kan matsalolin da suke fuskanta a rayuwar soyayyarsu. (2). Zuciyata Ce – Bilkisu Muhammad Littafin na ɗaya daga ciki...