Yawan Fitsari Ga Mai Ciki

Me Ke Kawo Yawan Fitsari Ga Mai Ciki?

Yawan fitsari ga mace mai ciki yana daga cikin abubuwan da yawanci suke damun mata tun daga farkon renon ciki har zuwa karshensa. Wasu mata suna samun damuwa sosai saboda yawan zuwa banɗaki, musamman da daddare ko lokacin da suke cikin tafiya. Amma shin, me ke janyo hakan? Shin alama ce ta matsala ko al’ada ce ta ciki?

Wannan rubutu zai bayyana muku dalilan da ke haddasa yawan fitsari ga mace mai ciki da kuma lokacin da ya kamata ta ziyarci  likita.



1. Sauyin Sinadarin Mace

A farkon watannin ciki, jikin mace yana fuskantar sauye-sauye na sinadarin hormone – musamman hormone HCG da progesterone. Wannan na iya sanya jinin ya ƙaru a jikin mace, kuma wannan karin jini yana kara nauyin dake cikin koda (kidneys), wanda ke tace ruwa da sauri – to hakan ke janyo yawan fitsari.



2. Karuwar Jinin Jiki

Lokacin da mace ke da ciki, jinin jikinta yana ƙaruwa sosai (kimanin 30-50%). Wannan karin jini yana shafar aikin kodar mace, domin suna buƙatar tace ruwa da cire gubobi daga jiki. Sakamakon haka, mace za ta dinga yawan jin fitsari.



3. Matsi daga Cikin Jariri

Yayin da jariri ke girma a cikin mahaifa (uterus), yana matse mafitsara (bladder). Wannan matsi yana rage sararin ajiyar fitsari, kuma yana sa mace ta rika jin buƙatar yin fitsari ko da bashi da yawa cikin mafitsarar.

A watanni na karshe na ciki (trimester na 3), wannan matsin yana ƙaruwa sosai, musamman idan kan jariri ya fara sauka ƙasa (engagement) domin haihuwa.



4. Shan Ruwa da Abinci Mai Yawan Ruwa

Mata masu ciki ana ba su shawarar su sha ruwa da yawa domin kada su kamu da bushewar jiki (dehydration). Wannan shan ruwa yana taimakawa ci gaban jariri da kuma lafiyar mahaifiya, amma yana kuma iya sa yawan fitsari.

Haka kuma, wasu kayan marmari kamar kankana, lemu, ayaba, ruwan kwakwa da dai sauransu na ƙunshe da ruwa da yawa, wanda ke ƙara yawan fitsari.



5. Rashin ƙarfin Mafitsara

Wasu mata na fama da rashin iya jure fitsari lokacin ciki (urinary incontinence). Wannan yana faruwa ne saboda raunin wasu tsokoki da ke kusa da mafitsara da mahaifa, musamman idan mace ta haihu sau da yawa to shima hakan na iya kawo yawan fitsari ga mai ciki.



6. Alamun Ciwon Infection

A wasu lokuta, yawan fitsari ga Mai ciki zai iya zama alamar ciwon mafitsara ko infection. Idan mace mai ciki tana jin:

  • Zafi ko kaikayi yayin fitsari

  • Jin nauyi a ƙasan ciki

  • Fitsarin da ke da wari

  • Jin ciwon baya

To, ya kamata ta gaggauta ganin likita saboda UTI na iya haifar da matsaloli ga ciki da jariri idan ba a kula da shi ba.



Yaushe Ne Ya Kamata A Damu?

Yawan fitsari a lokacin ciki al’ada ce. Amma idan kina da waɗannan alamomi, yana da kyau ki ga likita:

  • Jin zafi ko kaikayi yayin fitsari

  • Jini a cikin fitsari

  • Fitsari mai duhu ko wari

  • Yawan fitsari da ke zuwa da zazzabi ko ciwon ƙasan ciki

  • Rashin iya jure fitsari gaba ɗaya



Yadda Za a Taimakawa Kai

Ga wasu abubuwa domin mata masu ciki da ke fama da yawan fitsari:

  • Ki rage shan ruwa da dare domin guje wa tashi sau da dama cikin daddare

  • Ki daina shan abubuwan da ke tada fitsari kamar kayan zaki masu caffeine (kamar shayi ko coffee)

  • Ki ci abinci kadan-kadan a lokaci-lokaci domin rage matsi a cikin ciki

  • A rika motsa jiki masu sauki kamar Kegel exercises domin ƙarfafa tsokokin mafitsara



Kammalawa

Yawan fitsari ga mace mai ciki yawanci ba cuta ba ce – alama ce ta yadda jikinta ke aiki da kyau domin kula da jariri. Amma idan fitsarin yana da wasu alamomin haɗari, ko yana kawo damuwa sosai, to yana da kyau a nemi likita domin a tabbatar da lafiya.

Previous Post Next Post