Shekara Nawa Annabi Yayi A Madina

Shekara Nawa Annabi Yayi a Madina? 

Cikakken Bayani Akan Zaman Annabi Muhammadu (SAW) a Madina

A tarihin addinin musulunci, zaman Annabi Muhammadu (SAW) a Madina yana da matukar muhimmanci a cikin rayuwarsa da kuma cigaban Musuluncinma gabaki daya. Akwai tambaya da mutane da dama suke yawan yi: wato Shekara nawa Annabi yayi a Madina? Wannan tambaya tana da mahimmanci saboda abubuwan da suka faru a wannan lokaci sun kafa ginshikan addinin Musulunci har zuwa yau.


A cikin wannan cikakken bayani, za muyi bayani dai dai gwargwado akan shekara nawa Annabi yayi a Madina, abubuwan da suka faru a cikin wadannan shekaru, da yadda hakan ya taka muhimmiyar rawa a tarihin Musulunci.


Shekara Nawa Annabi Yayi a Madina?

Annabi Muhammadu (SAW) ya yi shekara goma (10) a Madina bayan hijirarsa daga Makka. Hijirarsa ta kasance a shekarar 622 Miladiyya (1 A.H - Shekara ta farko a kalanda ta Musulunci).


Wannan shekaru goma (10) da Annabi (SAW) yayi a Madina sun kasance cike da manyan abubuwan tarihi da suka sauya rayuwar Musulmi da musulunci gaba ɗaya.


Takaitaccen Tsari:

  • Hijira daga Makka zuwa Madina: Shekara ta 622 Miladiyya
  • Shekarun da ya yi a Madina: 10
  • Ranar wafatinsa: Ranar Litinin, 12 ga watan Rabi’ul Awwal, shekara ta 11 A.H


Dalilin Hijirar Annabi (SAW) Zuwa Madina

Kafin mu shiga cikakken bayani akan cigaban shekara nawa Annabi yayi a Madina post, ya kamata mu san dalilin da yasa Annabi (SAW) ya bar Makka zuwa Madina.


1. Tsanantar rashin goyon baya a Makkah 

Musulmai a Makka sun sha wahala, azaba, da kora daga mushrikai saboda sun karɓi Musulunci. Wannan yasa Annabi (SAW) ya yi hijira domin samun wuri mai kwanciyar hankali da damar yada addinin Allah cikin walwala.


2. Goyon Bayan Mutanen Madina

Mutanen Madina (Ansar) sun karɓi Musulunci a hannun manzo da sahabbansa, kuma suka bayar da goyon baya gare shi da sauran Musulmai. Wannan ne ya baiwa Musulmai damar su zauna a Madina.


Muhimman Abubuwan Da Suka Faru a Madina

A cikin shekara goma da Annabi yayi a Madina, abubuwa da dama sun faru wanda suka kafa ginshikin addinin Musulunci. Ga wasu daga cikinsu:


1. Gina Masallacin Annabi

Lokacin da Annabi ya isa Madina, abu na farko da ya fara yi shine gina masallaci, wanda har yanzu yana nan a Madina, wato Masallacin Annabi (Masjid Nabawi).


2. Kafa Yarjejeniyar Zaman Lafiya 

Annabi (SAW) ya kafa yarjejeniya tsakanin Musulmai da Yahudawan Madina don zaman lafiya. Wannan yarjejeniya ta kafa dokokin zamantakewa da hakkoki ga kowane bangare.


3. Yaki Domin Daukaka Kalmar Allah 

A cikin shekarun da Annabi (SAW) yayi a Madina, anyi wasu muhimman yakuna domin kare Musulunci daga barazanar makiya:

  • Yaƙin Badar (Shekara ta 2 A.H)
  • Yaƙin Uhud (Shekara ta 3 A.H)
  • Yaƙin Khandaq (Shekara ta 5 A.H)
  • Bude Makka (Shekara ta 8 A.H)

4. Fadada Addinin Musulunci

Annabi (SAW) ya aika da wasiku zuwa ga sarakunan duniya yana kiransu zuwa ga Musulunci, ciki har da Sarki Kisra na Farisa da Sarki Heraclius na Rumawa.


5. Hajjin Bankwana

A shekara ta 10 A.H, Annabi (SAW) ya yi Hajjin bankwana, inda ya yi hudubarsa ta karshe, wanda aka fi sani da Hudubar Bankwana.


Rayuwar Musulmai A Cikin Shekara 10 Na Zaman Annabi a Madina

A lokacin shekara goma da Annabi yayi a Madina, rayuwar Musulmai ta canza daga azabar da suka sha a Makka zuwa jindadi da walwala. An samu tsarin shari’a, tsarin zamantakewa, da kuma daidaito a tsakanin Musulmai da sauran mutanen Madina.


1. Kafa Daular Musulunci

Annabi (SAW) ya kafa Daular Musulunci a Madina, inda aka fara gudanar da mulki bisa tsarin Musulunci na gaskiya da adalci.


2. Yawaitar Zakka da Sadaqa

An kafa dokar zakka domin tallafa wa mabukata da kuma gina zamantakewa mai kyau a tsakanin Musulmai.


3. Karantarwa da Ilimi

Annabi (SAW) ya horas da sahabbansa akan ilimi da karantar da Al-Qur’ani, wanda hakan ya zamo ginshikin cigaban addini.


Yadda Zaman Annabi a Madina Ya Shafi Rayuwarmu Ta Yanzu

A yau, dukkan dokokin Musulunci da akidar addini suna da asali daga abubuwan da suka faru a cikin shekara goma da Annabi yayi a Madina. Wannan ya hada da:

  • Sallah (Cikakkiyar siffar Sallah)
  • Zakka
  • Azumi
  • Hajji
  • Dokokin zamantakewa da siyasa

Kammalawa

A takaice, idan ana tambaya shekara nawa Annabi yayi a Madina?, amsar ita ce shekara goma (10). Wadannan shekarun sun kasance mafiya muhimmanci a rayuwar a cigaban Musulunci gaba daya.


A Madina ne Musulunci ya kafa turbar da har yanzu muke rayuwa a cikinta. Akwai darussa masu yawa da za mu iya koya daga wannan lokaci, musamman yadda Annabi (SAW) ya yi amfani da hikima, hakuri, da adalci wajen kafa Daular Musulunci.


Allah ya kara mana fahimta da biyayya ga Annabi Muhammadu (SAW). Amin.

Previous Post Next Post