Amfanin Shan Ruwan Kanunfari

Amfanin Shan Ruwan Kanunfari:

A duniyar magungunan gargajiya da na zamani, akwai ganyayyaki da kayan ƙamshi da ke da matukar amfani wajen kiwon lafiya. Daya daga cikin shahararrun kayan ƙamshi da aka fi amfani da shi a gida da kuma wajen magani shi ne kanunfari. A kasar Hausa da dama, mutane da dama sun san da amfanin shan ruwan kanunfari wajen magance cututtuka daban-daban, amma har yanzu da yawa ba su san yadda ake cikakken amfani da shi ba.


A cikin wannan cikakken bayani, za mu binciko amfanin shan ruwan kanunfari, sinadaran da ke cikinsa, hanyoyin amfani da shi, da kuma shawarwari daga masana lafiya. Wannan rubutu zai taimaka maka wajen fahimtar yadda ruwan kanunfari zai iya zama sirrin samun lafiya a kullum.


Menene Kanunfari?

Kanunfari wani nau’in kayan ƙamshi ne wanda ke fitowa daga bishiyar da ake kira Siziya aroma. Wannan bishiya ta samo asali daga yankin Indonesia, amma yanzu ana noma ta a sassan duniya daban-daban. Ana amfani da kanunfari wajen dafa abinci, da kuma magani a al’adun gargajiya.


Kanunfari na dauke da sinadarai masu ƙarfi wanda ake kira eugenol, wanda ke da amfani wajen magance cututtuka da kuma kawar da radadin ciwon jiki.


Muhimman Abubuwan Dake Cikin Kanunfari

Ruwan kanunfari na dauke da wasu muhimman sinadarai masu matukar amfani ga lafiyar dan Adam. Wadanda sun hada da:

  • Eugenol – yana kashe ƙwayoyin cuta da rage radadi.
  • Vitamin C – don kara karfin garkuwar jiki.
  • Antioxidants – don yakar cututtukan da suka shafi tsufa da cutar daji.
  • Calcium, Iron, Magnesium – domin karfafa ƙashi da jini.
  • Fiber – don taimakawa narkewar abinci.

Amfanin Shan Ruwan Kanunfari Ga Lafiyar Dan Adam


1. Maganin Ciwon Ciki da Narkewar Abinci

Daya daga cikin sanannun amfanin shan ruwan kanunfari shine taimakawa wajen rage ciwon ciki da kuma saukaka narkewar abinci. Idan mutum na fama da ciwon ciki ko jin nauyin ciki bayan cin abinci, shan ruwan kanunfari na taimakawa hanji yadda ya kamata.


2. Taimakawa Wajen Rage Radadin Hakori

Eugenol dake cikin kanunfari nada matukar amfani wajen rage radadin hakori. Shan ruwan kanunfari ko kurkura da shi yana taimakawa wajen kashe kwayoyin cuta a cikin baki da kuma rage radadi.


3. Inganta Garkuwar Jiki

Saboda yawan sinadarin Vitamin C da antioxidants da ke cikin kanunfari, yana kara karfin garkuwar jiki domin yaki da cututtuka. Kuma AMFANIN SHAN RUWAN KANUNFARI yana taimakawa jikin dan Adam wajen kare kansa daga cututtuka kamar mura da zazzabi.


4. Taimakawa Lafiyar Jini

Wasu binciken kimiyya sun nuna cewa amfanin shan ruwan kanunfari ya hada da taimakawa wajen rage yawan cholesterol da kuma tsaftace jini. Wannan yana rage hadarin samun cututtuka kamar su hawan jini da ciwon zuciya.


5. Kara Karfin Maza

A al’adance, musamman a tsakanin Hausawa, wasu daga cikin amfanin shan ruwan kanunfari shine yana karfafa namiji a lokacin da kusantar iyali. Ruwan kanunfari na taimakawa wajen kara kuzari da karfin sha’awa.


6. Magance Matsalolin Numfashi

Ga wadanda ke fama da matsalar tari, mura ko kumburin makogwaro, shan ruwan kanunfari na iya taimakawa wajen rage wahalar numfashi. Haka kuma yana iya fitar da majina daga hanci da makogwaro.


7. Rage Ciwon Mara a Lokacin Al’ada

Ga mata masu fama da ciwon mara a lokacin al’ada (mensuration), shan ruwan kanunfari yana taimakawa wajen rage radadin saboda yana da sinadarai masu rage kumburi (anti-inflammatory properties).


8. Inganta Lafiyar Fata

Antioxidants da ke cikin kanunfari suna taimakawa wajen kare fata daga cututtuka da kumburi. Haka kuma, yana taimaka wa wajen cire kuraje da dai sauransu.


9. Magance Cututtukan Fata

Bincike ya nuna cewa amfanin shan ruwan kanunfari yana cire antimicrobial, wanda ke hana yaduwar cututtukan fata kamar fungi da bacteria. Idan ana son ƙara inganci, za a iya amfani da ruwan kanunfari don wanke wuraren da ke da matsalar fata.


10. Rage Nauyin Jiki

Ruwan kanunfari yana taimakawa wajen kara narkewar abinci da kuma rage yawan kitse a jiki ga mata masu kiba. Idan ana son rage kiba, yana da kyau a sha ruwan kanunfari musamman da safe kafin cin abinci.


Yadda Ake Hada Ruwan Kanunfari

Akwai hanyoyi da dama da ake bi don hadawa domin samun amfanin ruwan kanunfari:

Hanya ta Farko (Tafasawa)

  1. A dauki cokali 1 ko 2 na kanunfari.
  2. A tafasa cikin ruwa mai zafi na tsawon minti 10-15.
  3. A tace ruwan, a bar shi ya huce kadan sannan a sha.


Hanya ta Biyu (Soaking)

  1. A zuba kanunfari cikin ruwa mai dumi.
  2. A bar shi a cikin ruwa har tsawon awanni 5 zuwa 8 ko dare ɗaya.
  3. A tace ruwan sannan a sha da safe da kuma kafin kwanciya.


Hanya ta Uku (Da Zuma)

Domin kara dandano da kuma ƙarin fa’ida, ana iya haɗa ruwan kanunfari da zuma ko lemun tsami kafin sha.


Hanyoyin Kare Kai Daga Illolin Shan Ruwan Kanunfari

Koda yake amfanin shan ruwan kanunfari yana da yawa, yana da kyau a kiyaye wasu abubuwa:

  • Kada a sha fiye da kima, domin yawan eugenol na iya haifar da matsala ga hanta.
  • Mata masu juna biyu su tuntubi likita kafin amfani.
  • Mutanen da ke da cututtukan hanta ko masu daukar magunguna masu ƙarfi su tuntubi likita kafin amfani da shi a kai a kai.
  • Yara ƙanana kada su sha fiye da kima.


Bayanai Na Kimiyya Akan Amfanin Shan Ruwan Kanunfari

Binciken masana a fannin kimiyya ya tabbatar da cewa kanunfari na dauke da sinadarai masu yaki da cututtuka. Wani bincike daga National Institutes of Health (NIH) ya nuna cewa eugenol da ke cikin kanunfari yana da ƙarfi wajen yaki da ciwon daji da kuma rage kumburi a jiki. Haka kuma, wasu bincike sun nuna cewa yana taimakawa wajen daidaita yawan sukarin jini, musamman ga masu fama da ciwon suga.


Kammalawa

Amfanin shan ruwan kanunfari ya wuce tunanin mutane da dama. Tun daga rage radadin ciki, inganta garkuwar jiki, zuwa taimakawa lafiyar fata da jini, ruwan kanunfari na daga cikin magungunan gargajiya da za a iya dogaro da su idan aka yi amfani da su yadda ya kamata.


Sai dai kamar kowanne magani, ya kamata mutum ya bi hankali wajen amfani da shi kuma ya nemi shawarar likita idan yana da wata cuta ko yana amfani da wasu magungunan.

Previous Post Next Post