Addu'a Ga Mai Ciki

Addu'a Ga Mai Ciki:

A rayuwar kowane Musulmi, addu’a tana da matukar muhimmanci a kowane lokaci, musamman ga mace mai ciki. Lokacin rainon ciki lokaci ne na alfarma ga uwa, kuma yana bukatar addu’a, wato roƙo da neman kariya daga Ubangiji Allah. Domin lokaci ne da mace ke buƙatar kusanci da Ubangijinta domin samun kariya ga kanta da kuma jaririnta dake cikin cikinta.


Wannan cikakken post content nawa zai ba da gudunmawa akan addu'a ga mai ciki, nau’in addu’o’i da zaki iya yi, fa’idojin su, da yadda mace mai juna biyu za ta gudanar da rayuwarta domin kulawa da abinda take dauke dashi.


Muhimmancin Addu'a Ga Mai Ciki

Kowa dai yasan cewa addu’a wata hanya ce da Musulmi ke amfani domin neman taimako da tsari daga Allah akan dukkan bukatunsu. A lokacin renon ciki, akwai bukatar a nemi:

  • Kariya daga sharrin shaidanu
  • Kare kai daga cututtuka da miyagun abubuwa
  • Samun saukin renon ciki da wajen saukewa
  • Samun lafiyayyen jariri da nagartacciyar zuri’a

Addu’a ga mai ciki ba kawai don neman kariya bane, a'a har ma da kawo nutsuwa a zuciya da kwanciyar hankali ga mace mai ciki.


Lokutan da suka fi dacewa domin yin Addu’a Ga Mai Ciki

Ga wasu daga cikin lokutan da mace mai ciki ya kamata kar ta bari su wuce ba tayi addu'a ba.

  1. Bayan sallar farilla – saboda a lokacin addu’a tana karɓuwa yadda ya kamata.
  2. Lokacin sallar Tahajjud – lokacin da Allah yake saukowa kusa da bayinsa.
  3. Lokacin shan ruwa– neman albarka ga abincin da zai shigar da lafiya ga ciki bayan an kai azumi.
  4. Lokacin ziyarar asibiti ko ganin likita – neman kariya daga kowace illa.
  5. Kafin kwanciya barci – domin samun kariya daga sharrin shaidanu.


Addu'o’i Masu Kyau Ga Mai Ciki


1. Addu’ar Neman Sauƙi

اللّهُمَّ اجْعَلْ مَا فِي بَطْنِي خَلْقًا سَوِيًّا وَثَبِّتْهُ فِي رَحِمِي وَاخْرِجْهُ مِنِّي سَالِمًا سَوِيًّا وَاجْعَلْهُ مِنَ الصَّالِحِينَ.


“Ya Allah, Ka sanya abin da ke cikina ya kasance halitta mai kyau kuma Ka tabbatar dashi cikin mahaifata, Ka fitar da shi lafiya kuma Ka sanya shi cikin salihan bayi.”


2. Addu’ar Kariya Ga Ciki

أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّةِ مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لَامَّةٍ.


“Ina neman tsari daga kalmomin Allah cikakku daga dukkan shaidanu da mugayen halittu da dukkan mugayen idanu.”


3. Addu’ar Lafiyar Jariri

اللّهُمَّ اجْعَلْهُ ذَكِيًّا تَقِيًّا غَيْرَ شَقِيٍّ وَلَا غَوِيٍّ.


“Ya Allah, Ka sanya shi mai basira, mai tsoron Allah, kada Ka sanya shi cikin wawaye ko masu batanci.”


4. Addu’ar Sauƙin Haihuwa

رَبِّ هَوِّنْ عَلَيَّ مَا قَدَّرْتَ لِي مِنَ الْوِلَادَةِ وَاجْعَلْهَا وِلَادَةً سَهْلَةً مُبَارَكَةً.


“Ya Ubangijina, Ka sauƙaƙa mini abin da Ka ƙaddara daga haihuwa, Ka sanya haihuwa mai sauƙi a gareni kuma mai albarka.”


5. Karanta Surori Masu Albarka

Ga wasu daga cikin surorin da ake karantawa domin addu’a ga mai ciki:

  • Suratul Fatiha – domin albarka da neman lafiya.
  • Suratul Baqarah (Ayatul Kursiyyu) – domin kariya daga sharrin shaidanu.
  • Suratul Maryam – domin sauƙin haihuwa.
  • Suratul Inshirah – domin samun kwanciyar hankali da samun sauƙi.
  • Suratul Ikhlas, Falaq, da Nas – domin neman kariya daga kowane irin sharri.

Shawarwari Ga Mata Masu Ciki

  • Kada ki bar yin addu’a ko da kina cikin ƙunci ko rashin jin dadi.
  • Karanta Al-Qur’ani a kai a kai domin nutsuwa da kariya.
  • Yi amfani da lokuta masu albarka wajen yin addu’a kamar lokacin ruwan sama, cikin dare, da lokacin azumi.
  • Kar ki manta da addu’a ga mijinki da iyalinki gaba ɗaya.
  • Kiyi ƙoƙari ki zama cikin yanayi na tsafta da tsarki.

Kalaman Karin Gwiwa Ga Mai Ciki

  1. “Ki kasance da tawakkali, Allah yana tareda mai hakuri.”
  2. “Daukar ciki rahama ce daga Allah, kada ki ji tsoro.”
  3. “Addu’a tana sauya ƙaddara – ki roƙi Allah da yawa.”
  4. “Kowane lokaci na wahala yana tareda sauƙi, ki dogara ga Allah.”


Kammalawa

Addu'a ga mai ciki  abu ne mai matukar muhimmanci wanda ya kamata kowace mace mai ciki ta rika yi akai-akai. Yin addu’a yana ƙara ƙarfin gwiwa, yana kawar da damuwa, kuma yana sa mace mai ciki ta kasance cikin kulawar Allah.


Wajibi ne kowace mace mai ciki ta kasance tana karanta addu’o’i, domin ta kasance cikin nutsuwa, sannan ta dogara ga Allah domin shi isasshe ne, ta kasance cikin sanarwa Ubangiji dukkan bukatunki domin samun sauƙi da kariya wa kanta da jaririnki.


Allah Ya sauƙaƙa wa dukkan mata masu juna biyu, Ya raya musu abinda ke cikinsu, Ya basu haihuwa mai sauƙi, sannan ya basu lafiya. IDAN KIN HAIHU SHAFIN TSAMIYANOVELS YANA MIKI BARKA.

Previous Post Next Post