Maganin Girman Nono Na Budurwa

 Maganin Girman Nono na Budurwa –

A cikin wannan zamani, mata da yawa, musamman yan'mata, suna neman hanyoyi na kula da kai ko na magani domin kara girman nono. Wannan yana faruwa ne saboda dalilai na neman kyan gani, kwarin gwiwa, ko wani buri na musamman da mace ke da shi. A wannan rubutu mai taken maganin girman nono na budurwa, za mu yi bayani dalla-dalla akan magunguna na halitta da hanyoyi masu aminci da za su iya taimakawa wajen kara girman nono ga budurwa, ba tare da amfani da tiyata ko sinadarai masu illa ba.



Shin Yana Yiwuwa Kirji Ya Kara Girma Bayan Balagar Mace?

A’a, yawanci nono yana kara girma ne a lokacin balaga saboda hormones irin su estrogen da progesterone. Sai dai wasu matakan rayuwa ko sauyin hormones na iya shafar girman nono har bayan balaga. Haka kuma, akwai wasu abinci da motsa jiki da ake zaton na taimakawa wajen kara girman nono a hankali.



Magungunan Don Girman Nono na Budurwa

1. Man Zaitun (Olive Oil)

Man zaitun yana taimakawa wajen kara lafiyar fata da motsa jini a nono idan aka shafa shi tareda yin tausa. Hakan na yana iya sa nono ya kumbura kadan a hankali.


Yadda ake amfani dashi:

  • Ki dinga shafawa da safe da dare

  • A rika tausa nono na tsawon mintuna 10 zuwa 15

  • A cigaba da hakan na akalla sati biyu zuwa wata



2. Fenugreek (Hulba)

Fenugreek tana kunshe da sinadarai masu karfafa sinadarin estrogen, wanda ke da alaka da girman nono.


Yadda ake amfani da ita:

  • A tafasa hulba da ruwa a sha kofi daya a rana

  • Ko a hada garin hulba da ruwa ko man zaitun a shafa a nono gamida yin tausa

Lura: Hulba tana kara yawan nono a jikin wasu matan kuma tana taimakawa wajen cikar fata.

 


3. Soya beans (Waken Suya)

Soya beans na dauke da phytoestrogens, wanda suke kama da sinadarin estrogen wajen aiki. Wannan na iya taimakawa wajen a matsayin Maganin Girman Nono Na Budurwa ta hanyar cika fata da kumbura a hankali.


Yadda ake amfani dashi:

  • A rika cin waken soya, misali Awara ko kunun waken

  • A sha madarar soya (soya milk) kullum



4. Tafarnuwa da Zuma

Hadin tafarnuwa da zuma yana taimakawa wajen gyaran jiki gaba daya da kara kuzari. Yana kuma taimaka wa jini gudana sosai.


Yadda ake amfani:

  • Markada tafarnuwa

  • A hade da zuma

  • A rika sha sau daya ko biyu a rana



Motsa Jiki Don Kara Girman Nono

Koda yake motsa jiki baya kara yawan tsoka a nono (domin nono ba tsoka ba ne), amma yana kara lafiyar tsokokin kirji da fata wanda ke sa su tashi da kyau.


Wasu daga cikin motsa jikin sun hada da:

  • Push-ups

  • Chest presses

  • Wall press

  • Arm circles

A rika yin su sau 3 zuwa 4 a sati domin ingantaccen sakamako.



Abinci Masu Taimakawa Girman Nono

Wasu kalar abinci na daya cikin Maganin Girman Nono Na Budurwa masu taimakawa girman nono ta hanyar kara estrogen da lafiyar fata:

  • Madara

  • Ayaba

  • Avocado

  • Wake (legumes)

  • Masara (corn)

  • Kankana da lemo

  • Dabino

Tips: A guji shan kayan zaki da yawa da abubuwan da ke rage hormones na mace kamar caffeine da giya.

 


Magunguna Masu Sinadarin Estrogen (Amma Sai da Shawarar Likita)

Wasu magunguna da creams da ake saye a kasuwa na dauke da sinadarin estrogen ko progesterone. Amma yana da kyau a tuntubi likita kafin amfani da irin wadannan, domin suna iya haifar da illa ga lafiyar jiki ko hormone balance.



Tambayoyi da Ake Yawan Yi


1. Shin akwai magani da ke kara girman nono nan da nan?

A’a, babu magani ko cream da ke kara girman nono cikin dare daya. Duk wani sauyi da ake iya samu yana zuwa ne a hankali ta hanyar amfani da hanyoyi mafiya dacewa.


2. Shin hanyoyin nan suna da illa?

Idan aka yi amfani da su yadda ya kamata kuma ba tare da wuce gona da iri ba, yawancin hanyoyin ba su da illa. Amma duk da haka, ki kula da lafiyar jiki.


3. Ya kamata budurwa ta damu da girman nononta?

A'a. Girman nono da yawa baya bayyana kyawun mace. Abu mafi muhimmanci shine lafiya da kwarin gwiwa a jiki. Girman nono na dai dai misali yafi muhimmanci kan da yawa. Dan haka kar ki damu kanki



Kammalawa

Kara girman nono na budurwa abu ne da ke bukatar hakuri, kulawa da lafiyayyun hanyoyi. Yin amfani da man zaitun, hulba, motsa jiki da cin abinci mai kyau na iya taimakawa a hankali ba tare da hadarin illa ba. Duk wani Maganin Girman Nono Na Budurwa wanda bashi da tushe kada kiyi amfani dashi. yan magana sun ce zaman lafiya yafi zama dan sarki.

Idan kina bukatar karin bayani ko kina son hada magani da yafi dacewa da ke, ki rubuta a comment ko ki tuntube mu kai tsaye. Kada ki manta: kyau ba girman nono kadai ba ne, lafiya da kwarin gwiwarki su ne sirrin kyau.

Previous Post Next Post