Kalmomin Turanci da Fassarsu a Hausa –
Kalmomin Turanci Da Fassarar Hausa shine bayanin na yau. A wannan zamani da muka tsinci kanmu a ciki, yawan amfani da kalmomin Turanci yana ƙaruwa sosai a rayuwarmu ta yau da kullum, musamman a makarantu, ofisoshi, da kafafen sada zumunta. Amma da dama daga cikin masu amfani da harshen Hausa suna buƙatar fahimtar waɗannan kalmomi ta hanyar sauƙaƙa su zuwa Hausa. Wannan post ɗin zai kawo muku
jerin muhimman kalmomin Turanci da fassarar su a Hausa, domin sauƙaƙa karatu, sadarwa da kuma fahimta.
Fa'idar Sanin Kalmomin Turanci da Fassarsu a Hausa
- Sauƙaƙe fahimtar darussa a makaranta
- Taimakawa wajen fassarar wasiƙu, sakonni da takardu
- Inganta iya magana da rubutu a harshen Turanci
- Taimako ga dalibai dama masu neman ilimi gaba ɗaya
Jerin Kalmomin Turanci da Fassar a Hausa
Kalmomin Turanci |
Fassarar Hausa |
Book | Littafi |
Pen | Alƙalami |
School | Makaranta |
Chair | Kujera |
Table | Tebur |
Teacher | Malami/Malama |
Student | Dalibi/Daliba |
Love | Soyayya |
Water | Ruwa |
Food | Abinci |
House | Gida |
Door | Ƙofa |
Window | Taga |
Light | Haske |
Car | Mota |
Road | Hanya ko Titi |
Market | Kasuwa |
Money | Kuɗi |
Happy | Murna/Fara’a |
Sad | Baƙin ciki
|
Kalmomin Turanci Masu Alaƙa da Zamani
English Word |
Hausa Meaning |
Computer | Kwamfuta |
Phone | Waya |
Internet | Yanar Gizo |
Email | Imel |
App | Manhaja |
Social Media | Kafafen sada zumunta |
Screenshot | Hoton allo |
Download | Saukewa |
Upload | Ɗorawa |
Password | Kalmar sirri |
Kalmomin Soyayya da Zamantakewa
Turanci |
Fassarar Hausa |
Heart | Zuciya |
Feeling | Ji (ko jin zuciya) |
Relationship | Dangantaka |
Marriage | Aure |
Friend | Aboki/Abokiya |
Trust | Aminci |
Promise | Alkawari |
Kiss | Sumbata |
Hug | Runguma |
Smile | Murmushi |
Yadda zaka iya turanci a Sauƙaƙe
- Kayi amfani da dictionary apps ko kamar su English Hausa Translator. (Wannan shafi namu na aiki domin ɗora Translator domin fassara magana daga turanci zuwa Hausa)
- Rubuta sabbin kalmomi da fassara ka haddace da ƙwaƙwalwa
- Yin amfani da su a cikin hira da rubutu a koda yaushe ba tare da jin kunya ba
- Kalli fina-finan Hausa masu fassarar Turanci
- Karanta littattafan da ke dauke da fassarorin harsunan guda biyu
Kammalawa
Kalmomin Turanci da fassarar Hausa suna da matuƙar amfani ga kowa da kowa – daga dalibi zuwa malamai, daga ma’aikaci zuwa ga ɗan kasuwa. Wannan ilimi yana buɗe ƙofofin fahimta, sadarwa da ci gaba na yau da kullum. Muna fatan wannan jerin zai taimake ka wajen ƙara ilimi da inganta maganarka da harsunan biyu a lokaci guda.