Ayoyin Mallakar ;Ingantattun Ayoyi Domin Janyo Soyayyar Miji da Kulawa
Ayoyin mallaka namiji sune wasu ayoyi daga Alkur’ani mai girma da ake amfani da su domin janyo soyayya, kulawa da fahimta daga miji. A addinin musulunci, mun sani cewa Qur’ani yana cike da mu'ujiza iri daban daban, kuma karanta ayoyi tareda halastacciyar niyya nada matuƙar tasiri wajen kawo zaman lafiya da soyayya cikin zaman aure.
Me ake nufi da Ayoyin Mallakar Namiji?
Wadannan ayoyi ana karantawa ne domin:
- Janyo soyayyar miji
- Neman kulawa da fahimta
- Cika zuciyar miji da kaunar matarsa kurum
Ayoyin Mallakar Namiji Masu Karfi da Tasiri
1. Surah Yusuf – Aya ta 4
Arabic:
إِذْ قَالَ يُوسُفُ لِأَبِيهِ يَا أَبَتِ إِنِّي رَأَيْتُ أَحَدَ عَشَرَ كَوْكَبًا وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ رَأَيْتُهُمْ لِي سَاجِدِينَ
Tafsiri: Lokacin da Yusuf ya ce wa mahaifinsa: "Ya Abbana! Lalle na ga taurari guda goma sha ɗaya da rana da wata, na gan su suna yin sujada gare ni."
Amfani: Ki karanta sau 7 bayan sallar asuba da dare tare da ambato sunan mijinki da niyyar janyo kaunarsa da daukaka darajarki a idonsa.
2. Surah Taha – Aya ta 39
Arabic:
وَأَلْقَيْتُ عَلَيْكَ مَحَبَّةً مِّنِّي وَلِتُصْنَعَ عَلَىٰ عَيْنِي
Tafsiri: Kuma na sanya maka soyayya daga wurina, domin ka yi girma a gaban idona.
Amfani: Karanta sau 21 kowanne dare kafin kwanciya, da rokon Allah ya sanya soyayyarki a zuciyar mijinki.
3. Surah Al-Anfaal – Aya ta 63
Arabic:
وَأَلَّفَ بَيْنَ قُلُوبِهِمْ ۚ لَوْ أَنفَقْتَ مَا فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا مَّا أَلَّفْتَ بَيْنَ قُلُوبِهِمْ وَلَٰكِنَّ اللَّهَ أَلَّفَ بَيْنَهُمْ ۚ
Tafsiri: Kuma ya haɗa zukatansu. Da ka kashe duk abin da ke cikin duniya, ba za ka iya haɗa zukatansu ba, amma Allah ne ya haɗa su.
Amfani: Karanta sau 7 bayan kowace sallah tare da fatan samun haɗin kai da tunanin mijinki.
4. Surah Al-Qasas – Aya ta 26
Arabic:
إِنَّ خَيْرَ مَنِ اسْتَأْجَرْتَ الْقَوِيُّ الْأَمِينُ
Tafsiri: Lallai mafi alheri wanda za ka ɗauka aiki shi ne mai ƙarfi kuma amintacce.
Amfani: Ana karanta wannan aya da niyyar samun miji mai ƙarfi da aminci, ko kuma gyara halin miji da mayar da shi na gari da aminci a soyayya.
Yadda Ake Karanta Ayoyin Nan
- Karanta su lokacin da kike cikin tsarki bayan sallah ko da dare kafin kwanciya.
- Yi salati wa Annabi SAW kafin da bayan karatu.
- Ambaci sunan mijinki a addu’ar.
- Guji hada ayoyin da wani hali mara kyau ko sihiri.
Abubuwan Da Zasu Hana Tasirin Ayoyin Mallakar Namiji
- Rashin sallah da sabawa Allah.
- Yin karatu da zuciyar sharri ko cutarwa.
- Yin sihiri ko hadawa da asiri.
- Yin zina ko wani mugun nufi
Kammalawa
Ayoyin mallaka na namiji hanya ce mai matukar amfani da albarka don janyo soyayya da kulawa daga miji, ba tare da kin shiga haramun ko sihiri ba. Karanta ayoyin cikin tsafta kamar alwala, da tawakkali, kuma ki guji cutarwa. Wannan zai taimaka wajen samun kwanciyar hankali, soyayya da zaman lafiya a aurenki.