Abubuwan Da Suke Zubar Da Ciki

Abubuwan Da Suke Zubar Da Ciki

Abubuwan da Suke Zubar da Ciki – Dalilai da Hanyoyin Kariya

Abubuwan da suke zubar da ciki da yadda mace za ta kare kanta. Karanta wannan cikakken bayani a wannan gida namu mai albarka, domin kare lafiyarki a matsayin uwa dama jaririnki.



Gabatarwa

Zubar da ciki wani lamari ne mai matukar tayar da hankali da damuwa ga ma'aurata masu jiran haihuwa. Hakan yana faruwa ne lokacin da halittar ciki ta tsaya kafin lokacin haihuwa. A wannan rubutun, za mu bayyana abubuwan da ke haddasa zubar da ciki, yadda za a gane alamu, da matakan kariya da mace za ta ɗauka.



Menene Zubar da Ciki?

Zubar da ciki yana nufin rasa jariri a cikin makonni 20 na rainon ciki. Yawancin lokuta yana faruwa ne ba tare da an shirya ba, kuma hakan yana iya faruwa kafin mace ta ma gane tana dauke ciki.



Manyan Abubuwan da Suke Haddasa Zubar da Ciki

1. Matsalolin Kwayoyin Halitta

Idan akwai matsala a cikin kwayoyin chromosomes na jaririn da kike dauke dashi, hakan na iya janyo zubar da ciki. Wannan shine sanadi mafi yawa, kuma yana faruwa ne ta hanyar halitta.


2. Hawan Jini Mai Tsanani

Mace mai fama da ciwon hawan jini na iya fuskantar hadarin zubar da ciki, musamman idan bata samun magani akan lokaci.


3. Cututtuka

Cututtuka kamar su rubella, zazzabin cizon sauro, toxoplasmosis, syphilis, da kanjamau na iya kawo barazana ga lafiyar jariri a ciki.


4. Shan Magunguna Ba Tareda Shawarar Likita Ba

A wasu lokuta, mata na iya amfani da magunguna da ka iya shafar cigaban jariri, musamman a farkon wata uku na ciki. Wato shan magunguna barkatai.


5. Shan Giya da Taba Sigari

Halayen banza masu haɗari irin su shaye-shaye da shan taba sigari na daga cikin abubuwan da suke zubar da ciki. ko kuma shafar lafiyar ciki ba tareda an sani ba.


6. Aikin Wahala Mai Yawa

Matar da ke ɗauke da ciki ya kamata ta guji aikin da ke bukatar ɗaga nauyi ko yin aiki fiye da misali. Yin hakan na iya tayar da mahaifa da haddasa zubar da ciki.


7. Ciwon Suga

Na daya daga cikin abubuwan da suke zubar da ciki wato ciwon suga, musamman Idan ba a kula da shi yadda ya kamata ba, ciwon suga na iya shafar ciki har ma da haddasa zubar da ciki.


8. Rashin Daidaiton Sinadarin Hormones

Sinadarin hormone wanda aka fi sani da progesterone yana da matuƙar muhimmanci a farkon watanni. Idan ya yi ƙasa, ciki na iya zubewa. Yawanci wannan yana bukatar ziyarar likita.



Alamomin Zubewar Ciki

  • Fitar jini daga al'aura musamman ja ko mai duhu

  • Ciwon mara mai tsanani

  • Fitar da wani abu daga al’aura (kamar nama ko ruwa mai kauri)

  • Jin nauyi a ƙasan ciki ya daina

Idan kin fuskanci waɗannan alamomi, sai a gaggauta zuwa asibiti ko ganin likita.



Yadda Zaki Kare Juna Biyunki Daga Zubewa

  • Kula da lafiya tun kafin daukar ciki

  • Guji shan magani ba tareda shawarar likita ba

  • Kula da abinci mai gina jiki

  • Guji shaye-shaye da shan taba

  • Yin rigakafi kafin ciki (irin su rubella vaccine)

  • Kula da cututtuka kamar su suga da hawan jini

  • Guji yawan gajiya da ɗaga abu mai nauyi



Lokacin Neman Taimakon Likita

Idan kika fuskanci duk wani daga abubuwan da suke zubar da ciki da muka lissafa a sama ko kuma dama kin taba zubar da ciki sau da dama, to yana da kyau a tattauna da ƙwararren likita domin a gano matsala da kuma maganin ta.



Kammalawa

Abubuwan da suke zubar da ciki na iya faruwa ne saboda dalilai da dama, wasu daga ciki ba a iya kauce musu. Sai dai mace na iya ɗaukar matakai domin rage haɗarin hakan. Kula da lafiya, bin shawarar likita da kaucewa abubuwan haɗari na daga cikin hanyoyin kariya.

Previous Post Next Post