Free Hausa Novels Complete PDF

Free Hausa Novels Complete PDF– Inda Zaku Karanta Littafan Soyayya Cikin Sauki

Free Hausa Novels Complete PDF

A yau, karanta free Hausa Novels Complete na soyayya da sauran nau’ikan labarai ya zama abin sha’awa ga matasa da ma manya gaba ɗaya. Ko kunsan menene dalilin? Saboda littafan Hausa suna ɗauke da hikima, kuma suna dauke da nishaɗi da darussan rayuwa iri iri daban-daban masu ƙayatarwa. Wannan post nawa na yau da yardar mai duka zan tattauna dalla-dalla kan yadda zaka sami Free Hausa Novels Complete – wato cikakkun littafan Hausa kyauta, da inda zaka karanta su cikin sauƙi.

Me ake nufi da Free Hausa Novels Complete PDF?

Free Hausa Novels Complete na nufin cikakkun littafan Hausa da aka rubuta kuma ake bayarwa kyauta ba tare da biyan kudi ba. Wato wannan na iya haɗawa da:

1#Littafan Soyayya

2#Labaran ban dariya

3#Littafan addini da na darussa

4#Littafan tarihi da almara

Sakamakon yawan masu karatun Free Hausa Novels a yanar gizo hakan ne ya haifar da yaduwar shafukan da ke bayar da waɗannan novels cikin sauƙi.

Menene Karanta Hausa Novels Kyauta?

Nishaɗi da Ilimi: Littafan Hausa Novels suna kawo nishaɗi tareda darussa da zasu taimaka maka wajen gyaran rayuwa.

Sauƙin Samuwa: Zaka iya karanta novels a wayarka ko kwamfutarka a duk inda kake a fadin duniya.

Karfafa Harshen Hausa: Karanta littattafai yana ƙarfafa harshen Hausa da faɗaɗa amfani da kalmomi da jimloli masu ma’ana.

Rage Kashe Kuɗi: Saboda kyauta ne, ba sai ka kashe kuɗi ba kamar na siyan hardcopy a kasuwanni.

A Ina Zan Karanta Free Hausa Novels Complete?

Ga wasu shafuka yanar gizo da apps da zaka iya karanta ko sauke Free Hausa Novels Complete ko PDF kyauta:

1. Tsamiya Novels (www.tsamiyanovels.com.ng)


Wannan shafi nawa ne kuma ina iya bakin ƙoƙarina domin samar da cikakkun littafan Hausa na soyayya da sauran nau’ikan labarai. Ina sabunta littattafai akai-akai. Zaka iya saukewa ko karantawa kai tsaye a wannan blog nawa.

2. Wattpad Hausa Stories


Wattpad wani shafin sadarwa na yanar gizo ne wanda suke da application da ke ba masu rubutu damar wallafa labaransu. Yanzu haka akwai masu wallafa Hausa novels a can – duka a kyauta.

3. ArewaBooks


Wannan shafi yana da tarin littafan Hausa da zaka iya karantawa ko sauke su. Yanzu haka ana kara samun sababbin littattafai akai-akai.

4. Facebook Pages/Groups


Akwai shafuka da groups da dama a kafar sadarwa ta Facebook kamar:

__Hausa Novels Writers Forum

___Hausa Novels Exclusive

___Hausa Novels For You 

A nan, ana saka cikakkun novels kyauta kowace rana.

5. Google Drive & Telegram Groups


Wasu marubuta suna raba littattafansu ta hanyar links na Google Drive ko kuma a group na Telegram. Da zarar ka shiga irin waɗannan groups, zaka rika samun sababbin littattafai a kullum.

Wasu Daga Cikin Shahararrun Free Hausa Novels Complete ko ta PDF.

(1). Sirrin Zuciya

(2). Bana Ce Ba

(3). Rayuwata

(4). Hajiya Gwale

(5). So Da Kauna

(6). Ina Sonki Hajiya

(7). Sarkin Wuta

Wadannan Free Hausa Novels Complete dukkansu an rubuta su cikin salo na birgewa kuma kuna iya samunsu cikakku a shafukan da muka ambata.

Kammalawa

Free Hausa Novels Complete PDF hanya ce mai kyau ga masu sha’awar karatu don samun littattafai masu inganci ba tareda biyan kudi ba. Idan kai mai son soyayya ne, ko ka fi sha’awar almara da tarihi, to babu shakka zaka samu labaran da za su ɗauke hankalinka. Kada ka manta: littafi abokin rayuwa ne – karanta yau, ka ilmantu da gobenka!
Previous Post Next Post