Sharhin Littafin Kwai Cikin Kaya na Bilyn Abdul Kwai Cikin Kaya littafin marubuciya Bilyn Abdull ne yana ɗaya daga cikin fitattun littattafan Hausa da suka shahara a yan shekarun nan tsakanin masu karatu. Labarin kwai cikin kaya ya ƙunshi abubuwan da suka shafi soyayya, sirri, makirci, da kuma darussa masu ƙayatarwa. Bilyn Abdul ta wallafa littafin a shafukan yanar gizo kamar Kundintarihi.com.ng da Novels.com.ng, inda masu karatu ke samun damar karanta shi kyauta. Amma ayi sani cewa bani da tabbas cewa ita da kanta ta dora littafin a waɗannan kafofi illa iyaka Ni dai haka bincikena ya ganomin. Ƙarancin Labarin Kwai Cikin Kaya a shafukan sada zumunta Littafin Kwai Cikin Kaya yana bayar da labari ne akan rayuwar Jawaad, matashi mai kamun kai ga ladabi da biyayya, wanda ke fuskantar ƙalubale a rayuwarsa ta fuskar soyayyar dangantaka. A cikin labarin, marubuciyar ta bayyana yadda Jawaad ke mu'amala da Shahudah, wacce ta kasance kyakkyawar budurwa da ke da halaye masu ɗaure kai gamida ...
Read love, romance, adventure novels complete on our platform