Azabar Daren Farko: Abubuwan da Suke Haddasata da Yadda Ake Maganinsu Daren farko yana ɗaya daga cikin muhimman darare a rayuwar kowace sabuwar amarya, musamman idan budurwa ce wadda ba ta taɓa yin aure ba. Yawancin mata sukan ji tsoro ko damuwa game da abin da zai faru, wasu kuma suna jin labaran ciwo da Irin azabar daren farko da ke faruwa. A wannan blog namu mai taken azabar daren farko, zamu ƙaryata wasu abubuwan wanda ba gaskiya ba game da azabar daren farko, sannan mu bayyana dalilan dake haddasa ciwo a daren farkon wanda shine dai ake nufi da azabar daren farko ba wani abu ba. Idan kuka biyo mu ma har da yadda za'a rage duk wani radadi domin jindaɗin wannan dare mai muhimmanci ga sabon aure. Shin Azabar Daren Farko Dole Ce? A gaskiya, babu wata doka dake cewa dole sai daren farko ya kasance miki mai azaba ko samun wani ciwo yayin hulɗa da angonki. Sai dai kawai abinda muka sani shine wasu matan sukan fuskanci ɗan jin zafi, wasu kuma basa jin wani zafi sosai. Dalilan dake had...
Read love, romance, adventure novels complete on our platform